He Lifeng Ya Bukaci Amurka Da Ta Warware Takaddamar Cinikayya Da Sin Ta Hanyar Tattaunawa Da Hadin Gwiwa
Published: 11th, June 2025 GMT
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince, da nuna sahihanci wajen yin aiki tukuru, da aiwatar da gaskiya da kwazo wajen aiwatar da matsayar da aka cimma, ta yadda za a kai ga kare nasarorin da aka cimma ta hanyar shawarwari.
He, ya yi tsokacin ne yayin taron farko na shawarwari game da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ya gudana a ranakun Litinin da Talata a birnin Landan na Birtaniya, tare da jagoran tawagar Amurka a taron, sakataren baitul-mali Scott Bessent, da sakataren cinikayyar kasar Howard Lutnick da kuma wakilin cinikayyar kasar Jamieson Greer.
Yayin zaman tattaunawar, tsagin Amurka ya ce shawarwarin sun haifar da sakamako mai gamsarwa, kana an daidaita alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu, yayin da bangaren na Amurka ke fatan yin tafiya kafada da kafada da Sin, daidai da bukatun da shugabannin kasashen biyu suka amince, yayin zantawarsu ta wayar tarho, ta yadda za a tabbatar da nasarar aiwatar da matsayar da aka cimma a wannan taro. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai October 30, 2025
Manyan Labarai Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar October 30, 2025
Manyan Labarai Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15 October 30, 2025