Birnin Los Angeles Na Amurka Ya Rikice Yadda Ake Dauki Ba Dadi Tsakanin Al’ummar Jihar Da Jami’an Tsaro
Published: 11th, June 2025 GMT
Birnin Los Angeles na Amurka tana ci gaba da fuskantar tashe-tashe hankula kamar yadda zanga-zanga ta mamaye birnin
An ayyana dokar ta-baci a birnin Los Angeles na Amurka yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda kan batun gwamnatin kasar kan batun neman murkushe bakin haure.
Gavin Newsom ya dauki Trump a matsayin wani mai karya kundin tsarin mulki ta hanyar korar bakin haure da yawa ba tare da nuna bambanci ba, yana mai bayyana tura dakarun Marines da na National Guard a matsayin wani kara ruruta water tashin hankali na rashin hankali da zai kara tada zaune tsaye a birnin.
Bayan Donald Trump ya bayyana bakin haure a matsayin dabbobi da ke dauke da tutocin wasu kasashe, Trump ya yi alkawarin cewa ba zai kyale abin da ya kira ‘yan mamaya da bakin haure daga kasashe masu tasowa na duniya su mamaye birnin California ba kuma zai bankado masu ba da tallafi ga masu zanga-zangar a California.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
“Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.
“Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar su rika yin sintiri da sanya ido domin dakile ayyukan barayi da masu aikata laifuka a lunguna da sako na jihar,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp