Majalisar Dattijan Aljeriya Ta Soke Duk Wata Hulda Da Majalisar Dattijan Faransa
Published: 27th, February 2025 GMT
Majalisar Dattijan Aljeriya ta “dakatar da duk wata hulda da Majalisar Dattijan Faransa.
Majalisar al’ummar kasar, kwatankwacin majalisar dattijai a kasar Aljeriya, ta sanar da cewa ta “dakatar da dangantakarta” da majalisar dattawan Faransa, domin nuna adawa da ziyarar da shugabanta Gérard Larcher ya kai a ranakun Litinin da Talata a yankin yammacin Sahara.
Ziyarar ta biyo bayan wani gagarumin sauyi da shugaba Emmanuel Macron ya yi a watan Yulin shekarar 2024, inda ya nuna goyan baya ga shirin cin gashin kan yankin “karkashin ikon mulkin Moroko” wanda ya haifar da fushin Algiers.
Yankin da Spain ta yi wa mulkin mallaka na yammacin Sahara, wani yanki ne na hamada da Majalisar Dinkin Duniya ba ta yanke matsayi kansa ba, kashi 80% na kasar Maroko ne ke iko da shi, amma kungiyar ‘yan awaren Polisario, da ke samun goyon bayan Aljeriya, ta kwashe shekaru 50 tana fafatukar neman samun ‘yancinsa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dattijan da Majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Karamar Hukumar Bubura Ta Kai Tallafin Kayayyakin Abinci Cibiyar Gyaran Hali
Daga Usman Mohammed Zaria
Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar.
Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya kai ziyara ta duba cibiyar a baya.
A cewarsa, manufar bayar da tallafin ita ce don tallafa musu wajen kyautata rayuwarsu da kuma karfafa musu gwiwa su zama mutane nagari bayan sun fito daga gidan gyaran hali.
A nasa jawabin, jami’in da ke kula da cibiyar gyaran hali ta Babura, ASP Muhammad Ali, ya gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan karamci, yana mai cewa taimakon ya zo ne a lokacin da ake matuƙar buƙata.
A yayin hudubarsa ga fursunonin, Babban Limamin Babura, Imam Salisu Aliyu, ya shawarce su da su nemi gafarar Allah, su kuma kara kusanci gare Shi, tare da rungumar canji mai kyau.
Kayan tallafin da aka bayar sun haɗa da buhunan masara, gero, shinkafa, garin rogo, man gyada, sinadaran dandano, gidan sauro da maganin kwari.
Manyan baƙin da suka raka shugaban ƙaramar hukumar a lokacin ziyarar sun haɗa da Hakimin Babura, Sarkin Bai Ringim, Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha, jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin, CSP Abdu Jinjiri, da jami’in Hukumar Tsaro ta Civil Defence, CSC Sunusi Usman Chamo, da sauransu.