Rikicin Filato: An sake kone gidaje 96 a Mangu
Published: 11th, June 2025 GMT
Mahara sun kone gidaje akalla 96 a yankin Gyenbwas na gundumar Langai da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa maharan sun kuma kwashe musu kayan abinci da katifu da kuma shanu da sauran kayayyaki.
Alhaji Yakubu Umar, wanda kuma shi ne Madugun Langai ne ya shaida wa Aminiya hakan a ranar Talata.
Ya kuma ce bayan mutum biyun da aka kashe musu ranar Litinin, sun kuma kara samo gawar mutum daya a yankin, wanda hakan ya kai adadin mutanen da aka kashe yayin harin zuwa uku.
Mazauna yankin dai na zargin ’yan kabilar Birom da kai musu harin, kodayake su kuma sun musanta hakan.
A cewar Alhaji Yakubu, “Ba a taba yi mana irin wannan ta’addancin ba. maharan sun kone kayan amfani masu yawa ciki har da sutturu da kuma kayan abinci. Sannan sun sace kayayyakinmu na miliyoyin naira. Mu a gaskiya muna zaune da kowa lafiya a nan, shi ya sa ma harin ya yi matukar daure mana kai.
Daga nan sai ya yi kira da gwamnati da ta binciki harin domin ta hukunta wadanda ke da hannu a ciki sannan ta kai wa wadanda suka yi asara tallafi.
Ba mu muka kai harin ba – Birom
Sai dai Kungiyar Matasa Birom (BYM) ta karyata labarin kai harin, inda ta bayyana shi a matsayin na kanzon kurege.
Shugaban kungiyar, Dalyop Solomon, ya ce, “Jiya akwai mambobinmu uku da aka kai wa hari yayin da suke aiki a gonakinsu, wadanda yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Abin da muka sani kawai shi ne mutanenmu na cikin fargaba, kawai Fulani na fitowa ne saboda su samu dalilin kai mana hari.
“Amma ya kamata su sani, duk lokacin da suka kai mana hari, muna da ’yancin kare kanmu. Ba mamaki abin da ya faru ke nan. An zo kawo musu hari suka fatattaki maharan har zuwa maboyarsu, amma mu ba mu taba kai wa Fulani wani hari ba,” in ji Dalyop.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hari
এছাড়াও পড়ুন:
Yawan Mutanen Da Suka Rayukansu A Rikicin Lardin Suwaida Na Kasar Siriya Ya Kai 1,400
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Siriya ta tattara bayanan mutuwar mutane 1,400 a loardin Sweida na Siriya
Siriya, Faransa da Amurka sun sanar da wata taswirar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a Siriya, bayan tattaunawar da ba a taba ganin irinta ba a birnin Paris na Faransa, wadda ta hada ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Siriya Asaad al-Sheibani, da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot da manzon Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack.
Sanarwar ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron na bangarorin uku, ta tabbatar da goyon bayan shirin mika mulki ga gwamnatin kasar Siriya da karfafa hadin kan al’umma, musamman a birnin Sweida da ke arewa maso gabashin kasar Siriya, da hadin gwiwa wajen yaki da ta’addanci, da tabbatar da cewa babu wata jam’iyya da za ta kawo barazana ga zaman lafiyar yankin.
Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barak ya bayyana tattaunawar ta Paris a matsayin wani abin koyi na diflomasiyya mai tsauri da ke kawo karshen rikice-rikice, yana mai jaddada cewa kasarsa za ta ci gaba da hada kai da kawayenta wajen gina Siriya mai tsaro da hadin kai.