‘Yan Tawayen Sudan Sun Kai Hare-Hare Kan Ayarin Motocin Agaji A Kan Hanyarsu Ta Kai Agajin Jin Kai
Published: 10th, June 2025 GMT
Gwamnatin Sudan ta zargi ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa da kai hari kan ayarin motocin agaji kai a yankin Darfur
Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: “Dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan ayarin motocin agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur ta Arewa ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Sudan ta bayyana matukar bacin ranta tare da tofin Allah tsine da Allah wadai kan wannan mummunan lamari, tana mai jaddada cewa: “Yunkuri ne na ganganci na nufin toshe kungiyoyin agaji da dakile ayyukansu na kai kayan agaji ga fararen hula da suka makale a birnin El Fasher da sansanonin gudun hijira.”
Sanarwar ta ce “Hare-haren masu laifi sun yi sanadin lalata wasu manyan motocin Majalisar Dinkin Duniya, da kashe wasu masu gadi, da direbobi, da fararen hula, da kuma jikkata wasu jami’an tsaro da ke tare da ayarin motocin.”
Gwamnatin Sudan ta tabbatar da cewa: Harin ya saba wa dokokin jin kai na kasa da kasa, kuma kai tsaye da gangan ne aka niyyar illa ga kokarin da gwamnati take yi, tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa, na kai agajin gaggawa ga fararen hula da ke cikin bukata a halin yakin basasar kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Robert Malley: Harin Amurka A Kan Wuraren Nukiliyar Iran Babban Kure Ne
Tsohon wakilin Amurka na musamman a kan lamurran Iran Robert Malley, ya caccaki gwamnatin Donald Trump game da kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, lamarin da ya ce babban kure ne wanda kuma zai haifar da mummunan sakamako.
Robert Malley ya ce; ina tsammanin zabi na soja ba daidai ba ne bisa kowane irin dalili. Ba ya kula da matsalar da ke tattare da hakan sosai. Lamarin da zai haifar da rashin tabbas da sakamakon da ba za a iya tsammaninsa ba, ba kawai a cikin kwanaki masu zuwa, ko makonni ba, har ma watanni ko shekaru masu zuwa.
Don haka ina tsammanin cewa wannan shi ne zabi na kuskure da Trump ya dauka, in ji Robert Malley a wata hira da tashar labarai ta NBC ta Amurka.
Ya kuma kara da cewa, mutanen da suke tunanin cewa harin da Isra’ila da Amurka suka kaiwa zai haifar da tayar da kayar baya a cikin gida a Iran, shima wani kuren lissafi ne, saboda hare-haren da gwamnatocin kasashen waje ke kai wa ba wai kawai kan cibiyoyin nukiliyar Iran ba ne, har da asibitoci, da kuma kashe fararen hula.
Ya ce wasu abokansa Amurkawa ‘yan asalin kasar Iran gaya masa cewa, Iraniyawa suna kara samun hadin kai da kishin kasa a duk lokacin da aka kaiwa kasarsu farmaki.