A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Korea ta Kudu da su daukaka dangantakarsu zuwa matsayi na gaba ta yadda al’ummominsu za su kara amfana da ita da kawo tabbaci ga duniya mai cike da rashin tabbas, yayin da yake taya Lee Jae-myung murnar lashe zaben shugabancin kasar.

Tabbas kyakkayawar alaka tsakanin Sin da Korea ta kudu ta dace da yanayin da duniya ke ciki da muradun al’ummomin kasashen da ma tabbatuwar zaman lafiya a yankinsu da ma duniya baki daya.

A matsayinsu na makwabta, wadanda suka shafe shekaru 33 da kulla huldar diplomasiyya, kyakkyawar hulda tsakaninsu na da matukar muhimmanci musamman a irin wannan lokaci da duniya ke cike da hargitse da sauye-sauye da rashin tabbas.

Kamar yadda shugaba Xi ya bayyana, kasashen biyu makwabta ne da ba za a iya raba su ba. Don haka, ci gaban kowacce daga cikinsu, ci gaba ne ga dayar, haka ma akasinsa. Babu wanda yake kin cudanyar kasa da kasa, amma ya kamata, kowacce ’yantacciyar kasa ta kasance mai ra’ayinta na kashin kai da duba moriyarta da na makwabtanta yayin da take hulda da kasashen waje. Tarihi ya nuna yadda daidaituwar al’amura tsakanin bangarorin biyu ke samun tagomashi yayin da rashinsa ke haifar da koma baya. Yayin da Korea ta Kudu ta samu sabon shugaba, fatan ita ce zai jagoranci kasar wajen tsayawa kan ra’ayi na gaskiya da girmamawa da daidaito yayin cudanya da kasar Sin maimakon ba da dama ga masu wani ra’ayi na son kai don amfani da ita da zummar cimma burinsu. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Marasa Lafiya A Nasarawa Sun Koka Game Da Yajin Aikin Likitoci
  • El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai
  • Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
  • Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar