Masar Ta Yi Watsi Da Shawarar Cewa Ta Karbi Ragamar Gaza Na Wucin Gadi
Published: 27th, February 2025 GMT
Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.”
Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Tamim Khalaf yana cewa, “Duk wani ra’ayi ko shawarwari da suka saba wa matsayar Masar da Larabawa (a kan Gaza) an yi watsi da su kuma ba za a amince da su ba.
Kakakin ya nanata kiran da Masar ta yi na janyewar Isra’ila daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da kuma goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Mista Khalaf ya jaddada “dangantaka ta zahiri” tsakanin Gaza, yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye da kuma gabashin al-Quds, yana mai cewa suna wakiltar “yankin kasar Falasdinu mai cin gashin kanta kuma dole ne su kasance karkashin cikakken ikon mallakar Falasdinawa da gudanar da mulki.”
A ranar Talata ne, Yair Lapid na Isra’ila ya gabatar da wani shiri na Gaza bayan kawo karshen yakin.
A karkashin shirin nasa, Masar za ta karbi ragamar tafiyar da yankin da zarar an kammala yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
“Mafita ita ce Masar za ta dauki nauyin gudanar da Zirin Gaza na tsawon shekaru takwas tare da zabin tsawaita shi zuwa shekaru 15,” kamar yadda ya shaida wa kungiyar Haukish Foundation for Defence of Democracy (FDD) a Washington.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da sabon farmakin soji da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza.
Kasashen Biritaniya, Faransa, Italiya, Masar, Jordan, Qatar, Spain, duk sun yi tir da farmakin kan Gaza suna masu cewa zai kara dagula halin kunci da ake ciki.
Kungiyar tarayyar Turai, ta bakin Jami’ar kula da harkokin wajen ta, Kaja Kalas, ta yi kira da a sanyawa Isra’ila takunkumi domin matsa wa gwamnatin lamba ta kawo karshen hare-haren da take kaiwa Gaza, tana mai gargadin cewa al’amuran jin kai na kara ta’azzara.
“Hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza zasu haifar da mummunan sakamako game da halin da ake ciki da karin hasarar rayuka, da barna & hijira na jama’a,” in ji Kalas a kan X.
A jiya ne Sojojin Isra’ila suka kaddamar da sabon farmakin ta kasa mai manufar mamaye birnin Gaza bayan shafe makwanni ana kai hare-haren bama-bamai ba kakkautawa ba a kan wasu manyan gine-gine domin tilastawa Falasdinawa kauracewa gidajensu.
Farmakin ya zo ne jim kadan bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya gana da firaminista Benjamin Netanyahu a kusa da masallacin Al Aqsa da ke gabashin birnin Kudus da aka mamaye.
Tun da farko dai, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan yankunan Falasdinawa da ke mamaye, Francesca Albanese ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa birnin Gaza, tana mai cewa wani bangare ne na shirin Isra’ila na shafe Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci