IRGC : A yanzu makamman Iran masu linzami zasu iya harin Isra’ila daidai inda ake so
Published: 10th, June 2025 GMT
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa, a halin yanzu Jamhuriyar Musulunci za ta iya kai wa Isra’ila hari “daidai” inda ta ke so bayan samun bayanan sirri kan cibiyoyin nukiliyar gwamnatin Isra’ila.
Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wata wasika mai zuwa ga ministan leken asirin kasar, Esmail Khatib, inda ya taya shi murnar wani samame da aka kai a kwanan baya wanda ya bayar da damar samun bayyana sirrin Isra’ila da dama kan shirinta na nukiliya.
Wannan nasarar, ta baiwa hukumomin leken asirin Iran damar samun wasu tarin takardun Isra’ila da suka shafi makaman nukiliya, soji, tsaro da wasu wurare na kayayyakin more rayuwa.
Wuraren sun hada da wuraren da Isra’ila ke da shirin nukiliyar gwamnatin na boye, wanda aka ce ya baiwa Tel Aviv damar kera daruruwan makamai masu linzami da ba a san da su ba.
Janar Salami ya kara da cewa: “Wadannan takardun sirrin babu shakka zasu inganta tasirin kokarin da ake yi na hanzarta kawar da gwamnatin Sahayoniyawan da kuma kara sahihancin harin makamai masu linzami na Iran.
A shekarar da ta gabata Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari kan wasu muhimman wurare na Isra’ila a yankunan Falasdinawa da ta mamaye a wani gagarumin farmakin ramuwar gayya da ta gudanar a matsayin mayar da martani ga wuce gona da iri na gwamnatin Isra’ila.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.
Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.
A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.
Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp