Wang Yi Ya Gabatar Da Jawabi Albarkacin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa” Karo Na Farko Na MDD
Published: 11th, June 2025 GMT
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi ta bidiyo a gun bikin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa” karo na farko na MDD yau Talata.
Wang Yi ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin raya al’adu na duniya, inda ya ba da shawarar raya dabi’u na bai daya na dukkan bil’adama, da dora muhimmanci kan gado da kirkire-kirkire na wayewar kai, da karfafa mu’amala da hadin gwiwar al’adu tsakanin kasa da kasa, wadanda muhimmin kokari ne da kasar Sin ta yi don inganta tattaunawa tsakanin wayewar kai.
A shekarar 2024, babban taron MDD karo na 78, ya amince da kudurin da kasashe 83 ciki har da kasar Sin suka gabatar, na tabbatar da ranar 10 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa”. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA