Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Kaso Kusan 80% Sun Soki Musabbabin Barkewar Tarzoma A Amurka
Published: 12th, June 2025 GMT
Tarzoma ta barke a sassan Amurka da dama, har ta kai shugaban kasar ya bayar da umarnin kama gwamna. An kuma jibge dubban sojoji a birnin Los Angeles, kamar dai yadda jaridar “The Mirror” ta bayyana.
Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta fitar, ya nuna kaso mai yawa na Amurkawa sun damu da yiwuwar barkewar yakin basasa a kasar.
Bisa alkaluman jin ra’ayin al’umma, kaso 87 bisa dari na masu bayyana mahangarsu sun soki lamirin gwamnatin Amurka, bisa yadda take keta hakkokin bil’adama yayin da take tunkarar batun bakin haure. Kazalika, kaso 86 bisa dari na ganin batun bakin haure ya zamo wata babbar matsala ga tsarin jagorancin Amurka a cikin gida. Yayin da kaso 73.8 bisa dari ke ganin la’akari da tsanantar yanayin siyasa, da karuwar gibin tsakanin mawadata da talakawa, rayuwar Amurkawa marasa wadata tana kara tsananta. Har ma suna ganin an zuzuta zargin cewa wai bakin haure dake shiga Amurka ba bisa ka’ida ba sun fantsama a sassan kasar, yayin da kuma sabbin bakin haure dake shiga Amurka ke fuskantar kyama, sakamakon rikicin cikin gida dake ruruwa a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli.
Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja.
Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba.
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II“Za mu bincika asalin waɗannan kuɗaɗen da kuma dalilin da ya sa suke da su,” in ji Adebayo Okunola, shugaban cibiyar gyaran hali a Jihar Kwara.
Jami’an gwamnati sun kwashe kusan mutane 40 daga wuraren da suka haɗa da Tipper Garage, Offa Garage, Tank da Geri Alimi Roundabout.
Jami’an sun ce bakwai daga cikin waɗanda aka kama an taɓa kama su a baya, amma sun koma tituna bayan an sako su.
Kwamishinar jin daɗin jama’a ta jihar, Dakta Mariam Imam, ta ce adadin masu bara da aka kama ya ragu sosai idan aka kwatanta da na baya, inda ta ce suna sauya dabaru don su guje wa kama.
Ta roƙi jama’a da su daina ba wa masu bara kuɗi kai tsaye, su maida gudummawarsu ta hanyar wuraren ibada da gidajen marayu.
Jami’an gyaran hali sun ce za a tilasta wa waɗanda aka kama su yi aikin tsaftace tituna a matsayin horo da kuma darasi.
Wasu daga cikin masu barar sun roƙi gwamnati da ta tausaya musu, ba su da wata hanyar rayuwa sai bara.