HausaTv:
2025-06-22@17:34:01 GMT

Wani Kamfanin Kera Kayankin Aikin Likita Ya Gabatar Da Sabon Na’urar Tiyata

Published: 10th, June 2025 GMT

Wani kamfanin kera kayakin aikin likita mai zaman kansa a nan Tehran ya gabatar da wata na’ura mai aikin tiyata wanda kuma aka dora masa kayan aiki na zamani.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gabatara da wannan na’urar a kasuwar baje kolin kayakin aikin likita karo na 26TH wanda ke gudana a nan birnin Tehran.

Labarin ya kara da cewa samar da kayalin aikin likita wadanda suke tafiya da zamani, ya zama dole ne bayanda aka haka sayarwa kasar Iran irinsu daga waje.

Wannan hanin ya sa a dole daga cikin gida kwararru suka fara samar da kayakin aikin likita na zamani, don wadatar da asbitocin kasar daga sayan na waje, har ma tana sayarwa kasashen waje.

Mostafa Abdulgaffar shugaban kamfanin da ya samar da wannan na’urar yace : Na’urar za ta taimakawa lokitoci da wasu ayyuka masu muhimmanci dangane da marasa lafiyan da sukewa aiki, ta yadda likitocin ba za su yi kuskure na bata wani wuri a cikin jikin marasa lafiya wanda sukewa aiki ba.

Abdulgaffar ya kara da cewa kafin haka kasar Iran tana shigo da irin wadannan kayakin aikin likita ne daga kasashen Amurka, da Jamus. Amma bayan an dorawa kasar takunkuman tattalin arziki, sun dukufa a cikin gida saida suka samar da su. Suka kuma sami lasicin aiki da su a cikin asbitocin kasar da kuma saida su ga kasashen waje.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kayakin aikin likita

এছাড়াও পড়ুন:

Yunkurin Tauye Ci Gaban Fasahar Kera “Chips” Ta Sin Ba Zai Haifar Da Da Mai Ido Ba

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)
  • Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?
  • Firaministan Singapore: Jama’ar Sin Suna Da Kwarewar Kirkire-Kirkiren Fasahohi
  • Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Rasha Don Daukaka Amincewar Juna Ta Fuskar Siyasa Da Karfafa Muradun Juna
  • Za Mu Tabbatar Da Yin Aiki Da Ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani – Daurawa
  • Iran Ta Bayyana Sharaɗin Sasantawa Da Isra’ila – Ministan Harkokin Waje
  • An Kafa Fiye Da Kamfanonin Waje 24,000 A Sin Cikin Watanni 5 Na Farkon Bana
  • Katolika ta horar da shugabannin al’umma da na addini kan zaman lafiya
  • Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya
  • Yunkurin Tauye Ci Gaban Fasahar Kera “Chips” Ta Sin Ba Zai Haifar Da Da Mai Ido Ba