A yau ne aka gudanar da taron ministoci masu daidaita ayyukan da aka amince, a gun taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, a birnin Changsha dake lardin Hunan na kasar Sin, inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da taron, tare da karanta wasikar murnar bude bikin ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana ministan harkokin wajen kasar Kongo Brazaville Jean-Claude Gakosso, ya karanta wasikar murnar bude bikin ta shugaban kasarsa Denis Sassou Nguesso.

Taron ya samu halartar ministocin kasashe membobin kungiyar FOCAC, da wakilan kwamitin AU, da jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin, wadanda adadinsu ya zarce 100.

Wang Yi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Afirka su nuna goyon baya ga juna, da tabbatar da hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa a duniya, da ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, da yin kira da rika gudanar da cinikayya cikin ‘yanci a duniya, da ci gaba da samun moriyar juna, da kiyaye hadin gwiwar kasa da kasa, da samun bunkasuwa tare, da kiyaye adalci da tabbatar da odar kasa da kasa, da yin mu’amala da juna, da kuma sa kaimi ga tabbatar da bambance-bambancen wayewar kan duniya.

Minista Gakosso ya wakilci kasashen Afirka, inda ya bayyana cewa, ana maraba da shirye-shirye 10, na raya dangantakar abokantaka da shugaba Xi Jinping ya gabatar, da nuna goyon baya ga fatan hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2035, tare da fatan za a aiwatar da ayyukan da aka amince da su, a gun taron kolin FOCAC na birnin Beijing.

A hannu guda kuma, bangaren Afirka ya bayyana adawa da matakan kara buga harajin kwastam, da sanya takunkumi daga bangare daya, yana tsayawa tare da kasar Sin wajen tinkarar kalubale bai daya. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 

Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing.

Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800.

Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun ci gaba cikin sauye-sauye”, da “amfani da sarrafa sabbin fasahohi”, da kuma “kirkire-kirkire a bangaren kimiyya da fasaha da sauye-sauyen yanayin yaki”. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha
  • Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar