Leadership News Hausa:
2025-08-01@10:43:59 GMT

Gidauniyar Sarki Salman Ta Rab Tallafin Abinci Ga Mutane 2,450 A Kebbi

Published: 27th, February 2025 GMT

Gidauniyar Sarki Salman Ta Rab Tallafin Abinci Ga Mutane 2,450 A Kebbi

Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada. An gudanar da rabon kayan ne a ɗakin ajiyar abinci na gwamnatin jihar da ke Bulasa.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris a wajen rabon, ya gode wa gidauniyar bisa tallafin da ta ke bai wa mutanen jihar.

Amurka Da Rasha Sun Kammala Tattaunawar Kawo Ƙarshen Yakin Yukiren A Ƙasar Saudiyya Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya 

Ya ce wannan ba shi ne karo na farko da gidauniyar ke taimakawa ba, yana mai yabawa da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin su da ƙasar Saudi Arabiya, musamman kan ayyukan jin ƙai da aikin hajji. Gwamnatin jihar ta yaba da rawar da NEMA ta ke takawa wajen rabon tallafin.

Shugabar hukumar NEMA ta ƙasa, Hajiya Zubaida Umar, wadda Hajiya Fatima Kasim ta wakilta, ta ce gidauniyar Sarki Salman ta dauki tsawon lokaci tana bayar da irin wannan tallafi tun daga shekarar 2018 domin taimakawa marasa galihu a Nijeriya. Ta bayyana cewa bayan Kebbi, za a ci gaba da rabon kayan abinci a jihar Adamawa. NEMA ta gode wa gwamnatin tarayya da Gwamnatin Jihar Kebbi bisa haɗin kan da suka bayar wajen ganin an aiwatar da aikin cikin nasara.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa

Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe.

Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi.

Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China

Uwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu.

Ana iya tuna cewa, tun a daren ranar 13 ga watan Yuni zuwa wayewar gari 14 ga watan ne aka kashe fiye da mutum 100 a ƙauyen Yelwata, lamarin da ya janyo Allah wadai daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar.

Jihar Benuwe dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya, musamman rikicin manoma da makiyaya da kuma na ƙabilanci, wanda ke sanadiyyar salwantar rayuka da dama.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa
  • An Horas Da Mata 600 Kan Abincin Yara Mai Gina Jiki A Jigawa
  • Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kura
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Tallafin Miliyoyin Naira Ga Ƴan NURTW da Mahauta a Jigawa
  • Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza
  • Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000
  • Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
  • An Kaddamar da Makon MNCH na 2025, Ya Rarraba Fakitin Bayarwa 6,000, Kayan C/S 500
  • Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya
  • Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa