Iran Ta Fara Fidda Takardun Sirri Tsakanin HKI Da Hukumar IAEA
Published: 11th, June 2025 GMT
Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta fidda farkon bayanan sirra wanda ta samo daga HKI wadanda kuma suke tabbatar da dangantakar da hukumar IAEA take da shi da HKI da kuma sauran kasashen yamma da hukumomin tsaronsu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran tace a cikin bayanan da ma’aikatar ta wallafa ya zuwa yanzu ya nuna irin yadda hukumar IAEA take mika bayanan da ta samu daga cibiyoyin Nukliya na kasar Iran ga HKI.
Bayanan sun bayyana yadda hukumar ta IAEA take mikawa dukkan takardun sirri na shirin makamashin nukliya na kasar Iran ga makiyanta don su yi aiki a kai.
Banda HKI wadannan bayanan sun isa hannun hukumomi a kasashen yamma musamman Amurka.
Sannan sun tabbatar da cewa hukumar IAEA bata yin adalci a cikin ayyukanta. Amma daraktan hukumar Rafael Grossi ya bayyana cewa abinda gwamnatin Iran take fada dangane da shi da kuma hukumarsa ba gaskiya bane.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hukumar IAEA
এছাড়াও পড়ুন:
Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji
Duk da alƙawuran sojoji na kama fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji domin hukunta shi kan laifunan ta’addanci, har yanzu ɗan ta’addan bai daddara ba, a yayin da suke ci gaba da farautar sa shi da sauran manyan shugabannin ’yan bindiga da ke addabar ’yan Nijeriya.
Dakarun sojin da aka tura ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma da sauran ayyukan soji a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Tsakiya, sun yi nasarar halaka manyan jagororin bindiga da dama, ciki har da wasu na hannun daman Turji a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, amma dai har yanzu Turji, wanda ke gudun ɓuya bai shiga hannu ba, duk kuwa da neman sa ruwa a jallo da jami’an tsaro suka daɗe suna yi.
Daga lokacin da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa sababbin shugabannin tsaro zuwa yanzu, a tsawon shekara biyu, Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya yi alƙawari da barazana kimanin sau takwas, cewa za su kamo Turji su gurfanar da shi kan aikata “manyan laifuka” ga bil’adama.
Masana harkokin tsaro da aka zanta da su, sun bayyana cewa sojojin da aka tura domin samar da tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan suna da ƙarfi da ƙwarewar murƙushe Turji da duk wani ɗan ta’adda, idan har “akwai ƙarfin halin siyasa na tallafa musu.”
Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a ImoBinciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa Turji da yaransa da sauran ƙungiyoyin ’yan ta’adda na ci gaba da addabar mazauna ƙauyuka masu nisa, musamman a ƙananan hukumomi uku a Jihar Zamfara (Zurmi da Shinkafi da Gummi) inda ɓata-garin suke cin karensu babu babbaka.
ƙarin bincikenmu ya kuma gano cewa a halin yanzu sojoji suna sharar ƙananan hukumomi huɗu a jihar ta Zamfara, ciki har da Anka, inda dakarun ƙasa da na sama a ƙarƙarsin rundunar Operation Fansan Yamma ke gudanar da ayyuka na musamman.
A ziyarar da wakilinmu na harkokin tsaro ya kai Jihar Katsina kwanan nan ya lura cewa jami’an tsaro — sojojin sama da na ƙasa da na jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ’yan sa-kai da dai sauransu, suna ta ƙoƙarin ’yantar da wasu ƙananan hukumomi daga ’yan ta’adda kuma tuni aka samu nasara a ƙaramar Hukumar Batsari.
Wane Bello Turji?Bello Kachalla Turji, wanda aka fi sani da Turji, fitaccen shugaban ’yan ta’adda ne da ke addabar yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, musamman a jihohin Zamfara da Sakkwato da kuma Neja.
Turji, wanda aka haifa a shekarar 1994 a ƙaramar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara ya taso ne a matsayin makiyayi Bafulani ba tare da samun ilimi ba.
Ya taɓa yin zargin cewa wata ƙungiyar ’yan sa-kai mai samun goyon bayan jami’an tsaro ta kashe ’yan uwansa shida tare da sace wa danginsa dabbobi. A cewarsa, mahaifinsa ya yi yunƙurin kai ƙarar Sarkin Zurmi (wanda aka ba wa dabbobin da aka sace) amma abin ya ci tura.
Turji, wanda ya ƙara da cewa ’yan sa-kai sun kashe baffansa, ya shaida wa wakilinmu a wata hira a baya cewa, waɗannan abubuwa ne suka sa ya ɗauki makamai — dalilin da masu ruwa da tsaki suka yi watsi da shi.
A shekarar 2022 ɗan ta’addan ya jagoranci ’yan bindiga suka kai hare-hare a sassan Jihar Zamfara, inda suka kashe fararen hula kusan 200, ciki har da mata da ƙananan yara.
Ya yi ƙaurin suna wajen yin kisan kiyashi da hare-haren ta’addanci kan fararen hula da jami’an tsaro musamman a jihohin Zamfara da Sakkwato.
A watan Satumbar 2021, ’yan sa-kai sun kai hari kan wani masallaci a yankin Gwadabawa ta Jihar Zamfara, inda suka kashe mutum 11. A sakamaon haka, Turji ya jagoranci ’yan bindigarsa zuwa wata kasuwa a yankin Goronyo da ke Jihar Sakkwato, inda suka kashe fararen hula sama da 60.
A watan Disambar 2021, yaransa sun kai wa wata bas hari suka cinna mata wuta da fasinjojin cikinta. Mutum 30 ne suka mutu a mummunan harin a ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.
Shi ne kuma jagoran kisan gilla da aka yi wa mutane sama da mutane 200 a Jihar Zamfara a watan Janairu na 2022.
Turji ba ya ga maciiji da fitaccen shugaban ’yan bindiga nan mai suna Dogo Giɗe.
Ɓarnar ’yan bindiga a wata 6Bincikenmu ya nuna Turji da sauran kwamandojin ’yan bindigar da ba a kama ba da yaransu, sun kashe aƙalla mutum 66, ciki har da jami’an tsaro, a wata shida da suka gabata.
A ranar 30 ga Janairu, 2025, ’yan bindiga sun kashe mutum uku a garin Shinkafi a wani harin kwanton ɓauna a kusa da yankin ƙauran Namoda da ke Jihar Zamfara.
A ranar 2 ga Afrilu kuma, Bello Turji da mayaƙansa sun kashe manoma 11 a garin Lugu da ke ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.
Makonni biyu bayan nan, a ranar 15 ga Afrilu, suka kashe mutum ɗaya a ƙauyen Gabaken Mesa da ke ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, Jihar Zamfara.
Bayan mako guda, a ranar 22 ga Afrilu, suka kashe aƙalla mutum uku, ciki har da wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma ta Jihar Zamfara, a kan titin Anka zuwa Gusau.
Ranar 29 ga watan Mayu, 2025, ƙungiyar Turji ta kashe mutum huɗu a wani hari a ƙauyen Kungurki da ke ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.
Bayan kwana biyu ’yan bindiga sun yi kwanton ɓauna inda suka kashe mambobi uku na ‘Civilian JTF’ a ƙaramar hukumar a kan titin Gusau zuwa ƙauran Namoda.
A ranar 22 ga watan Yuni na wannan shekara ta 2025 kaɗai, ’yan bindiga sun kashe jami’an ‘Civilian JTF’ 40, tare da jami’an DSS huɗu da wani mai ba da bayanan sirri ga jami’an tsaro mai suna Bashar Maniya, a yankin Ruggar Chida da ke ƙaramar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara.
Alƙawuran sojoji sau 8Jami’an tsaro sun sha lasar takobi tare da ba wa ’yan Nijeriya tabbacin cewa dubun Bello Turji ta kusa cika — ko dai su kama shi da ransa ya fuskanci hukunci, ko kuma su aika shi lahira.
Haka kuma sun tsananta kai hare-hare kan maɓoyar ’yan ta’adda a cikin dazuka, inda suka yi nasarar halaka wasu mayaƙa da kwamandojojinsu, ciki har da muƙarraban Turji. Matsin lambar ta jiragen yaƙi da dakarun ƙasa da ke kai samame ta sa jagoran ɗan ta’addan ya shiga ɓuya.
Kwanan Turji ya kusa ƙarewa — Janar MusaA watan Satumbar 2024, Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta bayyana aniyarta ta kamowa tare da gurfanar da Turji a gaban ƙuliya domin ya girbi abin da ya shuka, tana mai alƙawarin kawo ƙarshen harajin da ’yan ta’adda suka ƙaƙaba wa manoma. Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya jaddada hakan ne a wani taron manema labarai, inda ya ce kwanan Turji ya kusa ƙarewa.
Don haka ya roƙi ’yan Nijeriya da su ba wa sojoji haɗin kai domin samun nasara, yana mai cewa da kuɗin da manoma ke biya kafin a bari su noma gonankinsu ’yan ta’addan suka dogara, wanda hakan ya nuna matsanancin takurar da ɓatagarin suka shiga. Haka kuma ya bayyana muhimmancin mutane su daina ba wa ’yan ta’addan bayanai game da motsin jami’an tsaro.
“Nan ba da jimawa ba za mu kamo shi. Harajin girbi da suke karɓa daga manoma zai zama tarihi. Dogaronsu da kuɗaɗen ya nuna irin matsin da suka shiga, amma ko sun samu kuɗin ma babu inda za su ji daɗinsa, saboda kuɗin jini ne. Shi ya sa yake da kyau jama’a su haɗa kai da jami’an tsaro domin su samu damar murƙushe ɓata-garin.
“Kada ku taimaka musu ko ku ba su bayanai kan ayyukan sojoji, domin wannan ita matsalar da muke fama da ita har yanzu a wasu al’ummomin, shi ya sa matsalar tsaro take ci gaba,” a cewar Janar Musa.
A watan Disambar 2024, tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Edward Buba, ya bayyana Turji a matsayin “matacce da ke tafiya kuma nan ba da jimawa ba za mu kawar da shi kamar saura dubban ’yan ta’adda da kwamandojinsu da muka riga aka halaka a bana.”
A ranar 19 ga Janairu, 2025, sojoji sun kai hari kan maɓoyar wani babban jagoran ta’addanci, inda suka lalata rumbun abincinsa, suka kashe ɗansa, amma ba su kama shi ba.
Haka kuma, a ranar 26 ga Janairu, 2025, Birgediya-Janar Opurum Timothy, Babban Kwamandan Rundunar Soja ta 1 da ke Gusau, Jihar Zamfara, ya bayyana Turji, wanda ya ce yake gudun ɓuya a matsayin, “Matsoracin da ya tsere ya bar mayaƙansa saboda matsin lambar da yake samu daga sojoji.” Janar Timothy ya kuma yi alƙawarin tsananta kai hare-hare kai tsaye kan sansanonin ’yan ta’addan.
A watan Afrilu, Janar Christopher Musa ya sake nanata matsayinsa, cewa sun kusa aika Bello Turji barzahu, yana mai musanta zargin da ake yi cewa sojoji sun rage yaƙar ɓarayin shanu da ’yan bindiga, inda ya jaddada cewa za su ci gaba da matsa ƙaimi domin kamo Turji.
Martanin ya zo ne bayan da ɗan ta’addan ya kashe manoma 11 a garin Lugu da ke Jihar Sakkwato, a lokacin da yake dawowa daga yawon Sallah zuwa wani yanki a ƙaramar Hukumar Isa ta jihar.
Babban Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwtar Tsaro na yanzu, Manjo-Janar Markus Kangye, ya ce za su ci gaba da halaka manyan ’yan ta’addan da ke ɓuya a dazuka. Ya ce, shi kuma “Bello Turji, lokaci ne kawai ya rage, za mu tura aika shi lahira inda zai iske sakamkon abin da ya aikata a gaban Mahaliccinsa.”
Ya ci gaba da cewa, “Mun kama manyan motoci maƙare da shanun da aka sato kuma mun ƙwato su, sa’annan muna ci gaba da farautar gawurtattun ’yan ta’adda. Mun halaka wasu da na bayyana sunayensu. Bello Turji kuma lokaci kawai ya rage.”
A watan Mayu, 2025, Turji ya sake tsira daga harin jiragen sama na sojoji a Jihar Sakkwato, inda dakarun suka kashe ɗaya daga cikin mataimakansa mai suna Shaudo Alku (wanda mazauna yankin ke kira Kallamu) da sauran ’yan ta’adda, a daura da makarantar firamare ta Tunfa a ƙaramar Hukumar Isa.
Alku da sauran ’yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a hanyarsu ta zuwa halartar wani taron kwamandojin ’yan bindiga da aka gayyace su daga Jamhuriyar Nijar.
Kwamandojin ’yan ta’adda da aka kasheDuk da yadda Turji ke zille wa sojoji, jami’an tsaro sun kashe wasu gawurtattun kwamandojin ’yan ta’adda, galibi ta hanyar hare-haren jiragen sama a kan maɓoyansu. Wasu kuma sun miƙa wuya ne saboda tsananin matsin lamba daga soji. A kwanan nan wani jagoran ’yan ta’adda mai suna Ibn Ali ya miƙa wuya tare da sallama makamansa ga sojoji a ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Borno.
A watan Yuni 2025 an kashe Kachalla Yello ɗanbokolo a ƙaramar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, a yankin da jami’an tsaro suka kashe Gwaska ɗanƙarami daga ƙauyen Shamushele na ƙaramar Hukumar Zurmi ta jihar a watan Nuwamba 2022.
Sauran manyan jagororin ’yan ta’addan da sojoji suka kashe tsakanin 2024 da 2025 sun haɗa da Dogo Saleh, wanda aka kashe a yankin Rijana, Jihar Kaduna a watan Maris 2025, yayin da aka kashe Halilu Sububu daga ƙauyen Sububu, ƙaramar Hukumar Maradu ta Jihar Zamfara a mahaifarsa.
A watan Maris ɗin ne kuma jami’an tsaro suka halaka Gero (Alhaji) da Alhaji Riga a dazukan Unguwar Goga ta Jihar Katsina, Kachalla Harisu kuma aka kashe shi a watan Afrilu a wani daji da ke iyaka da ƙananan hukumomin Safana da Dutsin-Ma a Jihar Katsina.
Jagoran ’yan ta’adda Tukur Sharme kuma an kashe shi ne a yankin Kachia, Jihar Kaduna a watan Satumba 2024, daga baya a watan Fabrairun 2025 kuma aka hakala Dogo Isa a ƙaramar hukumar, yayin da aka kashe Dogo Maikasuwa, wanda aka fi sani da Dogo Millionaire, a yankin Chikun, ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.
A watan Fabrairu 2025, an kashe Kamilu Chiroma (Buzaro) a tsaunin Dargaza, unguwar Maidabino B, ƙaramar Hukumar ɗanmusa ta Jihar Katsina. An kuma kashe wani babban kwamandan ’yan ta’adda, ɗan Mudale, a garin Keta da ke ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara a watan Maris 2025.
Manyan’yan ta’adda da ke ɓuyaBaya ga Turji wanda ɗan asalin ƙauyen Fakai ne a Jihar Zamfara, yawancin sauran kwamandojin ’yan bindiga da suka ko suke ci gaba da addabar al’umma sun shiga ɓuya, a yayin da sojoji suka sanya tukuicin Naira miliyan biyar a kan kowane ɗaya daga cikinsu ga duk wanda zai iya bayar da gudunmawa wajen kama su ko kashe su. Waɗannan sun haɗa da:
• Ɓaleri daga ƙaramar Hukumar Shinkafi.
• Ado Aliero daga ƙauyen Yankuzo a ƙaramar Hukumar Tsafe.
• Ali Kachalla (Ali Kawaje) daga ƙauyen Kuyambara, ƙaramar Hukumar Maru.
• Sani ɗangote daga ƙauyen Dumbarum, ƙaramar Hukumar Zurmi.
• Nasanda daga ƙauyen Kwashaɓawa a ƙaramar Hukumar Zurmi.
• Umaru ɗan Nijeriya da daga ƙauyen Rafi, ƙaramar Hukumar Gusau.
• Da kuma Nagala daga gundumar Mada ta ƙaramar Hukumar Maru, duk a Jihar Zamfara.
• Daga Jihar Katsina akwai Leko daga ƙauyen Mozoj, ƙaramar Hukumar Matazu.
• Dogo Nahali daga ƙauyen ’Yar Tsamiyar, ƙaramar Hukumar ƙanƙara, Katsina.
• Monore daga ƙauyen ’Yantumaki, ƙaramar Hukumar ɗanMusa.
• Isiya Garwa daga ƙauyen Kamfanin Daudawa, ƙaramar Hukumar Faskari.
• Sai Mamudu Tainange Abu Radde, ɗan-ɗa, da Sani Gurgu — duk daga ƙauyen Baranda a ƙaramar Hukumar Batsari.
• Akwai kuma Nagona daga Angwan Galadima a ƙaramar Hukumar Isa, Jihar Sakkwato.
Akwai buƙatar ƙarfin hali — MasanaAbdullahi Garba, wani ƙwararre a fannin leƙen asiri da yaƙi da ta’addanci, ya danganta ci gaban ayyukan manyan ’yan ta’adda da rashin ƙarfin hali. Ya buƙaci Shugaban ƙasa
Bola Ahmed Tinubu da babban hafsan tsaro da su bayar da umarni ga kwamandojin soji don kawar da ’yan ta’adda daga dazuka.
Garba wanda ya bayyana cewa suna da ƙarfin yin hakan cikin ’yan watanni, ya yi zargin cewa wasu mutane suna amfana daga rashin tsaro da ke faruwa, wanda ke hana ƙoƙarin daƙile matsalar.
Matakan da ba na soji ba na da muhimmaci — MasanaChukwuma Ume, wani ƙwararre a fannin gyara a harkar tsaro ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa tsakanin sojoji da ’yan sanda a yankunan da aka ƙwato daga ’yan ta’adda, yana mai ba da shawarar yin amfani da matakan da ba na soji ba don hana mutanen yankunan shiga ƙungiyoyin masu laifi.
Duk da cewa ya amince da muhimmancin amfani da matakan soji, amma ya bayyana cewa tasirinsu na gajeren lokaci ne. Saboda haka ya ce mafita ta dogon lokaci ita ce magance tushen matsaloli kamar nuna wariya, rashin daidaito a tsakanin al’umma, talauci, rashin aikin yi, da kuma rashin ɗa’a daga jami’an tsaro, waɗanda za a iya warware su ba tare da amfani da tashin hankali ba.
Ume ya bayyana kashe manyan shugabannin ’yan bindiga a matsayin nasara ta wucin gadi, yana mai kira sojoji da su ci gaba da kasancewa a yankunan da aka ’yanta daga miyagun, don kada su samu damar sake mamayewa.
Ya kuma yi kira da a ƙara rarraba arziƙin ƙasa da ƙara buɗe damarmaki domin al’umma su samu abin dogaro da kai, ayyukan kiwon lafiya, ilimi, da sauransu a matsayin hanyoyin magance matsalolin gaba ɗaya.
Masanin ya bayyana cewa ko da an bayar da duk waɗannan damamraki, wasu mutane na iya ƙin gyaruwa, don haka ba za a yi watsi da amfani da matakin soji ba gaba ɗaya.