Leadership News Hausa:
2025-07-28@07:47:58 GMT

Guguwa Za Ta Sa Kasashen Sin Da Afirka Su Kara Rike Hannayen Juna

Published: 11th, June 2025 GMT

Guguwa Za Ta Sa Kasashen Sin Da Afirka Su Kara Rike Hannayen Juna

Don haka, a cikin sanarwar da aka fitar a wannan karo, kasashen Afirka sun nuna yabo kan jajircewar kasar Sin, da kuma kudurin da kasar ta dauka na kare adalci, da kuma ingancin tsare-tsaren tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Har ila yau, kasar Sin ita ma ta nuna godiya ga kasashen Afirka, kan yadda suke bin ka’idojin kare ‘yancin kai, da adalci, tare da tsayawa kan matsaya guda wajen fuskantar matsin lamba da aka sanya musu.

Hakika idan mun tantance kwarin gwiwar Sin da Afirka, za mu ga da farko ya zo daga dangantakarsu mai dorewa ta hadin gwiwa da juna. Za mu iya daukar misalin bangaren ciniki: daga shekarar 2000, lokacin da aka kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, zuwa bara, yawan ciniki tsakanin Sin da Afirka ya karu daga dalar Amurka biliyan 13.92 zuwa dalar Amurka biliyan 295.56, wanda ya karu da fiye da sau 20. Kana kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki ta Afirka mafi girma a duniya tsawon shekaru 16 a jere. Sa’an nan, a watanni hudu na farkon bana, darajar ciniki tsakanin Sin da Afirka ta kai dalar Amurka biliyan 103.1, adadin da ya karu da kashi 8.1% bisa na makamancin lokacin bara. Kana idan mun duba nan gaba, a cikin wasikar taya murna ga taron da aka gudanar a birnin Changsha, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, za a aiwatar da shirin ba da damar yafe harajin fito 100% ga kasashe 53 dake nahiyar Afirka masu huldar diflomasiyya da kasar Sin, kana a sa’i daya kuma, zai samar da karin sauki ga kasashe mafin karancin tattalin arziki a Afirka don su fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin. Wadannan alkaluman da na ambata sun nuna cewa, daga a baya har zuwa yau, da kuma nan gaba, hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Afirka na kara habaka. Wannan ya nuna yadda amintattun abokan hadin gwiwa ya kamata su kasance tare da juna.

Ko ta yaya wasu kasashe ke tayar da hankali a duniya, za mu iya ganin wannan hoto: Sin da Afirka, aminai na kwarai, suna tsayawa tare da juna, rike da hannayen juna, a kokarin tabbatar da ci gaban kasashensu na bai daya. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Burtaniya Zata Fara Jefawa Falasdinawa Abinci Daga Sama

Firai ministan kasar Burtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa ya fara tuntubar wasu kasashen turai kan nshirin jefawa Falasdinawa abinci daga sama tare da taimakon kasar Jordan.

Shafin yanar gizo na Arab News ya nakalto Starmer yana fadar haka a yau Asanar ya kuma kara da cewa ya yi magana da kasashen Faransa da Jamus kan wannan shirin.

Labarin ya kara da cewa banda jefa masu abinci kasashen zasu sauka su dauki marasa lafiya musamman yara kanana don jinyarsu..

Tun kimani watanni 4 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta rufe kofofin shiga zirin gaza ta kuma hana shigowar abinci da magunguna, da nufin kashe dukkan falasdinawa kimani miliyon biyu a Gza, don ginawa yahudawa matsugunai a yankin.

Tun fara yakinn tufanul aksa a ranar 07 ga watan Octoban shekara 2023 ya zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa fiye da dubu 60 a yayinda wasu fiye da dubu 150 suka ji rauni.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bakaken Fatar Amruka Da Suke Yin Hijira Zuwa Afirka  Suna Karuwa
  • Zanga-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Falasdinu A Birnin Tunis Fadar Mulkin Kasar Tunusiya
  • Burtaniya Zata Fara Jefawa Falasdinawa Abinci Daga Sama
  • Tallafin Lafiya: Ƙungiyar Rotary Ta Raba Kayan Haihuwa kyauta Ga Mata Masu Juna Biyu  A Kaduna
  • Gwamnatin Tarayya Na Shirin Dakatar Da Shigo Da Kifi Daga Ketare
  • Miliyoyin Al’ummar Yemen Sun Fito Taron Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Falasdinawa
  • Shugaban Kasar Ukraine Ya Nuna Sha’awar Ganawa Da Shugaban Kasar Rasha
  • Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Xi Jinping Ya Karbi Takardun Nadi Daga Sabbin Jakadun Kasashen Waje
  • An Amince Da Biranen Kasar Sin 9 A Matsayin Biranen Dausayi Na Kasa Da Kasa