WHO : har yanzu kyandar biri na da matukar hadari ga duniya
Published: 10th, June 2025 GMT
Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Dr. Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa har yanzu cutar kyandar biri wato Mpox na kasancewa mai matukar hadari a faɗin duniya.
Wannan sanarwa ta biyo bayan taro na hudu da kwamitin gaggawa na kiyaye dokokin harkar lafiya na duniya IHR ya gudanar a ranar 5 ga Yunin 2025, domin nazarin halin da ake ciki game da yaduwar cutar ta Mpox.
Hukumar ta kuma ce duk da cewa an samu ci gaba a wasu kasashe wajen fuskantar cutar, kwamitin ya gargadi shugaban hukumar da cewa lamarin har yanzu babbar barazana ce ga lafiyar jama’a a duniya.
Kwamitin ya danganta wannan da ci gaba da karuwar yawan masu kamuwa da cutar, ciki har da karin wadanda suka kamu da cutar a yankin Yammacin Afirka, da kuma yiyuwar yaduwar cutar ba tare da an gano ta ba a wasu kasashen da ke wajen nahiyar Afirka.
Sanarwar ta kuma ce har yanzu akwai kalubale wajen gudanar da aikin dakile cutar, ciki har da matsaloli a fannin lura da yaduwar cutar da gwaje-gwaje.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe mutum 15 a sabbin hare-hare a Filato
Rayukan aƙalla mutum 15 sun salwanta a wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato.
Shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, ya shaida wa manema labarai cewa, a daren ranar Talata ce aka kashe mutum bakwai a kauyen Bwai sai kuma mutane takwas a kauyen Chinchim duk a ƙaramar hukumar ta Mangu.
Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a ZariyaWannan lamari na daga cikin sabbin hare-hare da tashin hankali da ke ci gaba da faruwa a yankin a wannan makon tsakanin yan kabilar Mwaghavul da Fulani.
Hare-hare daban-daban guda uku da suka faru a yankin ƙaramar hukumar Mangu a ranar Litinin da Talata, sun biyo bayan jerin hare-hare da ramuwar gayya da ake kyautata zaton sun fara ne yayin da mutane ke aikin haƙar ma’adinai a yankin da ke da arzikin Tin, a cewar shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ta ruwaito Emmanuel Bala yana cewa, “Makiyayan Fulani Musulmai masu yawo da dabbobi sun daɗe suna samun saɓani da manoma da suke zaune a Jihar Filato — waɗanda mafi yawansu Kiristoci ne — kan rikicin mallakar fili da albarkatun ƙasa.”.
Ya ƙara da cewa hare-haren da ake kai wa a yankin sau da yawa na da nasaba da bambancin ƙabila da addini, wanda ke haifar da hare-haren ramuwar gayya marasa kakkautawa.
“Watanni da suka wuce, wasu mazauna yankin na aikin haƙar ma’adinai, sai aka kai musu hari da adduna, kodayake babu wanda ya mutu a harin farko.
“Amma bayan jerin ramuwar gayya da martani, an kai hare-hare uku a ranar Litinin da Talata, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 20,” in ji Bala.
Wani jami’in Red Cross ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu cikin sa’o’i 24 a harin Chinchin, yana mai cewa adadinsu na iya kai wa 21.