Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Tace Sinadarin Uranium
Published: 10th, June 2025 GMT
Iran ta bayyana cewa: Tace sinadarin Uranium wani bangare ne na bunkasa masana’antar nukiliya kuma ba zata amince kan tattaunawa ko yin sulhu kansa ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Sarrafa sinadarin Uranium wani bangare ne na masana’antar nukiliya, kuma batu ne da ba za a tattaunawa kansa ko yin sulhu kansa ba, kasancewarsa masana’antar cikin gida ne kuma an shefe tsawon shekaru da dama ana sarrafa shi a cikin kasa, sakamakon kokarin da masana kimiyya suka yi.
A cikin taron manema labarai na mako-mako, Baqa’i ya yi ishara da abubuwan da ke faruwa a duniya a halin yanzu, yana mai jaddada cewa: “abin da ba za a yi watsi da shi ba shi ne halin da ake ciki mai radadi a Falastinu da aka mamaye,” yana mai cewa: Ana ci gaba da “aiwatar da kisan kare dangi a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa suka yi shiru.”
Ya jaddada cewa, amfani da veto da Amurka ta yi a kan wani kuduri na neman kawo karshen kisan kare dangi a Gaza, lamari ne da ke jaddada goyon bayan Amurka da taimakonta ga gwamnatin yahudawan sahayaoniyya.
Kakakin ya yi ishara da shahadar fararen hula sama da 150 da ba su ji ba ba su gani ba a ‘yan kwanakin nan, yana mai jaddada cewa; “Dole ne kasashen duniya su dauki kwararan matakai don kawo karshen wannan bala’i na jin kai.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta yi matukar Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kasar Iran, tare da jefa bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar kasar, dake karkashin kulawar hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA a takaice.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, lokacin da yake tsokaci kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyi uku na nukiliyar kasar Iran. Jami’in ya ce matakin Amurka ya yi matukar keta makasudi, da ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa, ya kuma ruruta yanayin rashin tabbas da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Daga nan sai jami’in ya ce Sin na kira ga sassa masu ruwa da tsaki a tashin hankalin dake wakana, musamman ma Isra’ila, da su gaggauta cimma matsayar dakatar da bude wuta, tare da tabbatar da tsaron rayukan fararen hula, da fara tattaunawa da shawarwari. Ya ce Sin a shirye take, ta yi aiki da sauran kasashe wajen aiwatar da matakan tabbatar da adalci, da aiki tukuru wajen dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp