Aminiya:
2025-07-27@23:31:43 GMT

A hanzarta kwangilar yashe Madatsar Ruwa ta Alau — Gwamnatin Borno

Published: 11th, June 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanzarta ɗaukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam ɗin Alau da ya haifar da ambaliya a bara.

Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam ɗin amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya fuskantar mummunar ambaliya.

Dalilin da Nijeriya ke fuskantar tsaiko wajen karɓar rancen $5bn daga Saudiyya Saudiyya za ta fara bayar da bizar Umara

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin tsaro na Jihar Borno, Farfesa Umar Tar da harkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa an bayar da kwantaragin kuma minista ya je ya ƙaddamar da aikin.

“Har yanzu ba mu ga ’yan kwangila sun zo domin fara aikin ba kuma yanzu ga damuna ta riga ta sauka.

“Idan ba a yi aikin nan da wuri ba to idan ruwa ya zo ya yi halinsa to lallai za a samu matsala.

“Ya kamata a ce an yashe ruwan saboda irin cunkushewar da ya yi. Idan aka yashe shi to ko ruwa ya zo da yawa ba zai ambaliya ba,” in ji Farfesa Tar.

A damunar bara ne dai madatsar ruwa ta Alou Dam ta cika ta tunbatsa inda ta kuma karye, wani abu da ya janyo ambaliyar ruwa da ya haddasa asarar rayuka da ta dukiyoyi a birnin Maiduguri.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jihar Borno Madatsar Ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Za mu ba da damar shigar da kayan agaji a Gaza — Isra’ila

Isra’ila ta ce za ta bai wa ayarin Majalisar Dinkin Duniya damar shiga Gaza domin raba kayan agaji da magani, bayan makonni na matsin lamba daga hukumomi da kasashen duniya.

Sanarwar da rundunar sojin Isra’ila ta fitar ranar Asabar, ta ce ta bayar damar komawa jefa kayan agajin ta jiragen sama – abin da aka ce bai wadatar ba, baya ga hadarin da ke tattare da shi.

Super Falcons ta lashe gasar WAFCON karo na 10 bayan doke Maroko ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark

Rundunar sojin ta ce ta fara aiwatar da wasu jerin matakai na inganta kai agajin a yankunan da ke da tarin jama’a

Hakan dai na zuwa ne a yayin da Isra’ilar ke sci gaba da fuskantar matsin lamba daga hukumomi da kasashen duniya da ke bayyana damuwa kan al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza za su fada cikin mummunan bala’in yunwa.

A bayan nan dai Isra’ila ta takaita shigar da kayan agajin da magunguna tsawon watanni ga al’ummar yankin su miliyan biyu, a yayin da take ci gaba da musanta abin da ta kira ikirarin haddasa yunwa ga al’ummar ta Gaza da gangan.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito kafofin Falasdinawa suna tabbatar da ci gaba da aikin jefa kayan agajin ta sama, a yankin arewacin Gaza.

Tun daga farkon watan Maris ne Isra’ila ta dakatar da bayar da dukkanin kayan agajin, amma ta bayar da damar bayarwa amma da sababbin sharuda a watan Mayu.

Isra’ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza

Aƙalla mutane 25 ne suka mutu a wasu hare-hare ta sama da kuma ta ƙasa da sojojin Isra’ila suka kai cikin dare a yankin Gaza.

Jami’an kiwon lafiya a asibitin Shifa da aka kai gawarwakin mutanen, sun ce mafi yawancinsu an kashe sune ta hanyar harbi da bindiga, a lokacin da suke dakon isowar motocin kayan agaji ta mashigar Zikim.

Wannan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da tattaunawar da ake yi don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ta fuskanci koma baya, sakamakon yadda Amurka da Isra’ila suka janye wakilansu a ranar Alhamis.

A ranar Juma’a ce firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce gwamnatinsa na duba yuwuwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu da Hamas, kalaman da ke zuwa dai-dai lokacin da jami’in Hamas ke cewa ana saran a mako mai zuwa ne za su ci gaba da tattaunawa kan batun.

Ƙasashen Masar da Qatar waɗanda ke shiga tsakani a tattaunawar tare da Amurka, sun ce an dakatar da tattaunawar ce na ɗan ƙaramin lokaci, kuma za a ci gaba da ita duk da yake ba su bayyana zuwa wane lokaci ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsohon shugaban jami’ar Kashere ya rasu a Abuja
  • Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP
  • Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani
  • Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa
  • Za mu ba da damar shigar da kayan agaji a Gaza — Isra’ila
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Kaddamar Da Dashen Itatuwa Na Bana
  • Rasha Ta Sha Alwashin Mayar Wa Da Nato Martani Mai Tsanani Idan Ta Kai Ma Ta Hari
  • Asusun NADF, OCP Da Gwamnatin Katsina Sun Kaddamar Da Noman Hekta 50
  • Manyan Nasarorin Da Dakta Dantsoho Ya Samar Tun Darewarsa Shugabancin NPA
  • Gwamnatin Tarayya Na Shirin Dakatar Da Shigo Da Kifi Daga Ketare