Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram A Jihar Yobe
Published: 10th, June 2025 GMT
A wani samame da aka kai a Mallamfatori, cikin Karamar Hukumar Abadam, sojojin sun gano ƙarin gawarwakin ‘yan ta’adda da kuma tarin makamai.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47, babura, harsasai masu yawa, ma’ajin harsasai, bututun roka, bom na hannu, rediyon hannu da wasu kayayyakin soji.
Rundunar sojin ta ce waɗannan hare-hare na baya-bayan nan na nuna ƙwazon da ake yi wajen murƙushe Boko Haram da ISWAP tare da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa Maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram Kwamanda
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa
Kakakin Brigade ya bayyana cewa ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen magance duk wani yunkuri na sojojin Nijeriya wajen aikata aikin da bai dace ba, tare da tabbatar da da’a, da bin doka da oda.
Ya yi nuni da cewa ba za a iya jure duk wani nau’i na rashin da’a a tsakanin ma’aikatanta ba.
Ya kuma ba jama’a tabbacin cewa sakamakon binciken zai fito fili domin tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma adalci.
Rundunar ta kuma bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu, su guji yada jita-jita, ko kuma shiga ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, tare da yin alkawarin tabbatar da martabarta da kuma bautar kasa.
A halin da ake ciki dai, kisan ya janyo cece-ku-ce a tsakanin mazauna yankin da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’Adama, wadanda ke kira da a gudanar da bincike na gaskiya ba tare da nuna son kai ba kan lamarin da ya kai ga mutuwarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp