Leadership News Hausa:
2025-07-29@09:44:42 GMT

Zan Ci Gaba Da Ɓata Wa Masu Sukar Tinubu Rai Da Ayyuka – Wike

Published: 12th, June 2025 GMT

Zan Ci Gaba Da Ɓata Wa Masu Sukar Tinubu Rai Da Ayyuka – Wike

Ya ce ya fahimci haka ne bayan kallon wani shiri a talabijin inda ya ga wasu mutane na nuna rashin jin daɗi.

Wike ya ce wannan baƙin ciki na su shi ne ke ba shi ƙwarin gwiwa.

“Na ji wani irin abu a zuciyata, sai na kunna talabijin. A nan ne na gano cewa wasu na cikin baƙin ciki saboda abubuwan alheri da ake yi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Yanzu da na gane suna cikin baƙin ciki, zan ci gaba da sanya musu ƙarin ciwon zuciya. Farin cikinmu na ƙaruwa ne da jin haushinsu. Wannan shi ne sabon aikina na ci gaba da sa musu hawan jini.”

Wike ya yi raha da cewa yayin da suke cikin fushi da damuwa, shi da shugaban ƙasa za su ci gaba da dariya da gudanar da ayyuka.

Ya gode wa Shugaba Tinubu bisa jagorantar abin da ya kira “juyin juya hali na ci gaba.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Ayyuka

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki

Shugaban kungiyar Hamass ya bayyana cewa HKI da gwamnatin kasar Amurka sun janye daga tattaunawa tsakaninsu da kungiyar ne don sake komawa yaki har zuwa lokacinda zasu shafe falasdinawa a gaza.

Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran ya nakalto Kkalilul Hayya, yana fadar haka a wani jawabin da aka watsa a tashoshin talabijin nay au Litinin.

Alhayya ya bayyana cewa akwai ci gaba a tattaunawar tsagaiuta wuta tsakanin kungiyar da HKI da kuma Amurka, amma janyewar HKI da kuma Amurka a wannan tattaunawar wata dasisa ce don ci gaba da kissan kiyashi a gaza.

Ya ce: masu shiga tsakanin sun tabbatar da cewa akwai ci gaba a tattaunawar da ake yi a doha, sai dai sun janye ne don samun lokacinda da zasu gaggauta kissan Falasdinawa a Gaza, don cimma mummunan manufofinsu a gaza.

Dangane da rabon kayakin agaji wanda HKI da Amurska suka shira kuma Alhayya ya yi allawadai da shi ya kuma kara da cewa cibiyoyin bada agajin tarko ne na kara kissan Falasdinawa a Gaza.

Ya kara da cewa shirin GHF na Amurka da kuma HKI shiri ne na kissan karin Falasdinawa bayan sun sanyasu cikin yunwa na kimani watanni biyu kafin su fara rabon abinda suke kira agaji.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki
  • Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu
  • Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 
  • Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kiran Cewa; Ina Masu Fafatukar Kare Hakkin Dan Adam Suke A Bala’in Gaza?
  • Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa
  • Sin Ta Yi Kira Da A Ci Gaba Da Himmatuwa Wajen Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana
  • Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
  •  Gaza: Ana Ci Gaba Da Samun Shahidai Da Yunwa Take Kashewa A Gaza