Aminiya:
2025-11-02@03:38:04 GMT

Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a 2027 – Amaechi

Published: 11th, June 2025 GMT

Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya shirya yin haɗaka da wasu ’yan siyasa domin ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

A wata hira da ya yi da BBC, Amaechi ya ce matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar ne babban dalilin da ya sa ake buƙatar sabuwar haɗaka a siyasa.

Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Rikicin Filato: An sake kone gidaje 96 a Mangu

Ko da yake bai tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa ba, sai dai ya ce komai zai bayyana nan da wani lokaci.

“Lokaci ne kawai zai nuna,” in ji shi.

Wannan bayani na zuws ne ƙasa da wata guda bayan shugabannin APC sun ayyana Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya tilo na jam’iyyar a 2027.

Amma Amaechi ya ce har yanzu yana kishin jam’iyyar APC, amma hakan ba yana nufin ya amince da duk abin da gwamnati ke yi ba.

“Idan gwamnati na gazawa wajen ciyar da ƙasa gaba, ba wai saboda kana cikin jam’iyyar sai ka yarda da komai ba. Ka san hakan ba daidai ba ne,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa abu mai kyau shi ne faɗa wa gwamnati gaskiya da kuma bayyana abin da ’yan ƙasa ke buƙata.

Amaechi ya nuna damuwarsa kan yadda yunwa da talauci ke ƙara tsananta a ƙasar, inda ya bayar da misali da wani abin da ya faru da shi.

“Mutane na mutuwa. Mutane na fama da yunwa. Ni kaina na fara jin tasirin yunwar nan,” in ji shi.

“Gaskiya ita ce, ni ma ina jin yunwar nan.”

Ya ce ko da yake mutane na ganin yana da hali, amma matsin tattalin arziƙin yana shafar kowa.

Ya ce bai yanke shawarar tsayawa takara ba tukuna, amma yana ganin zai iya kawo sauyi.

“Tabbas, ina ganin zan iya bayar da gudunmawa mai ma’ana,” in ji shi.

Amaechi ya ce yana tattaunawa da wasu ’yan Najeriya da ke ganin ƙasar na tafiya bisa kuskure domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kawo sauyi.

Ana kuma samu rahotanni cewa fitattun ’yan adawa kamar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na Labour Party su ma na shirin kafa haɗaka kafin zaɓen 2027.

Hakazalika, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya goyi bayan Tinubu a 2023, kwanan nan ya ce ana ƙoƙarin kafa wata haɗaka da za ta iya ƙalubalantar Shugaba Tinubu.

Sai dai a ’yan watannin nan, wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa sun koma APC, abin da ke tayar da hankali cewa Najeriya na iya koma wa tsarin jam’iyya ɗaya.

Amaechi ya ce ƙasar ta tsaya cak, kuma ana ci gaba da tuntuɓa kan hanyoyin gyara halin da ake ciki.

“Muna tunanin cewa idan muka haɗa kai muka ci zaɓe, tabbas ƙasar za ta fuskanci sauyi,” in ji shi.

Da yake tunawa da lokacin da yake Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Amaechi ya ce a wancan lokacin yara miliyan 10 ne ba sa zuwa makaranta, amma yanzu sun ƙara yawa.

Ya kuma nuna damuwa game da taɓarɓarewa tsaro a ƙasar.

“Rigimar manoma da makiyaya na nan, satar mutane don karɓar kuɗin fansa ma na ci gaba da faruwa,” in ji shi.

Amaechi ya alaƙanta matsalolin Boko Haram da sauran rikice-rikice da yunwa da matsin rayuwa.

“Na daɗe ina cewa Boko Haram ba rikicin addini ba ne. Da yawa daga cikin waɗanda ke ciki na shiga ne saboda yunwa da tsananin buƙata,” in ji shi.

Najeriya ta shafe sama da shekara 15 tana fama da rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

A watannin baya ma hare-haren mayaƙan sun ƙara tsananta, duk da iƙirarin gwamnati na cewa ta yi nasara.

Har ila yau, ’yan bindiga na ci gaba da addabar ƙauyuka a Zamfara, Sakkwato, Katsina da Kaduna, inda suka tilasta wa dubban manoma barin gonakinsu.

A cikin wani rahoton Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa, ta ce mutane 570 ne suka mutu a watan Afrilu 2025 kaɗai.

Wasu na ganin cewa ƙarfin siyasar Amaechi ya ragu, tun bayan rasa madafun iko musamman a Jihar Ribas.

Amma ya ƙaryata hakan.

“Ku je Fatakwal ku tambaya, daga filin jirgin sama ma, za ku ga ni da idonku,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Matsin Rayuwa yunwa Zaɓe Amaechi ya ce

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

 

Ya kuma bayyana cewa kasar Sin wuri ne mai kyau ga harkokin zuba jari ga ‘yan kasuwa na duniya. Ya ce hadin gwiwa da kasar Sin yana nufin hadin gwiwa da damammaki, imani da kasar Sin yana nufin imani da kyakkyawar makoma, zuba jari a kasar Sin yana nufin zuba jari mai riba ta dogon zango.(Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi October 31, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
  • Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP
  • Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • ACF ta mara wa gwamnatin Tinubu baya