Iran Tana Daga Cikin Kasashe 3 A Nahiyar Asiya Wadanda Suke Da Lamunin Samun Isasshen Abinci
Published: 10th, June 2025 GMT
Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Iran ta bayyana cewa kasar a halin ayanzu tana daga cikin kasashe uku na gaba a kan abinda ya shafi samun isasshen abinci mai lafiya da kuma wadatacce a cikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan kiwon lafiya Muhammad Reza Zafarkandi yana fadar haka a jiya litinin a taron raya ranar abinci da duniya wanda aka gudanar a dakin taro na hukumar gidajen radio da talabijin a nan birnin Tehran.
Ministan ya kara da cewa, samun abinci mai gina jiki da kuma bada sinadaran da jiki yake bukata yana daga cikin abubuwan da suke bada lafiya ga jiki.
Har’ila yau wannan yana kwantar da hankalin mutanen ko wace kasa wacce take da wannan matsayin na samar da abinci da kuma lamunin lafiyar abincin.
Ministan ya ce akwai kamfanonin samar da abinci a cikin kasar kimani 17,000 wadanda ma’aikatar take kula da dukkan abincin da suke samarwa, don tabbatar da lafiyansu da kuma ingancinsu kafin su sayarwa mutane.
Sannan ma’aikatar tana da dakunan bincike har 450 wadanda suke gwada lafiyar abincin da wadannan kamfanoni suke samarwa a duk fadin kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati.
Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala.
NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makarantaShirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan irin damar da masu yi wa kasa hidima suke da ita a garuruwan da aka tura su.
Domin sauke shirin, latsa nan