Isra’ila ta sake kashe Falasdinawa a wurin rabon tallafi
Published: 10th, June 2025 GMT
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla mutum 20 ne sukayi shahada a wani sabon harin da sojojin Isra’ila suka kai a lokacin da ake rabon abinci a Gaza.
Shaidun gani da ido sun ce sojojin Isra’ila sun bude wuta da safiyar Talatar nan, kan Falasdinawa da za su karbi kayayyaki a tsakiyar Gaza a wani wuri da ke karkashin gidauniyar agaji ta Gaza (GHF).
Jami’an Falasdinawa sun kara da cewa sama da mutane 120 ne suka jikkata a harin na Isra’ila.
Harin na baya-bayan nan ya zo ne sa’o’i bayan da sojojin Isra’ila suka kashe Falasdinawa 14 da suka taru a wajen wata cibiyar GHF da ke kudancin Rafah.
Kisan na yau ya sanya adadin wadanda sukayi shahada a wajen rabon abinci a Gaza sanadin hare-haren Isra’ila zuwa 110 tun ranar 27 ga watan Mayu, a tsarin rabon abincin na GHF da ke samun goyon bayan Isra’ila da Amurka.
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa ne ke sukan tsarin rabon tallafin wanda wasu ke dangantawa da tarkon mutuwa.
Halin da ake ciki na jin kai a Gaza ya kai intaha inda kungiyoyi musamman MDD ke bayyana shi da mafi muni a duniya.
Tun bayan fara yakin kisan kare dangi da Isra’ila ta kaddamar a ranar 7 ga Oktoba, 2023, adadin Falasdinawa da sukayi shahada ya kai 54,927, yawancinsu mata da kananan yara, sannan wasu kusan 126,615 sun jikkata.
A watan Nuwamba 2024, Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ba da sammacin kama Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministansa na soja Yoav Gallant, bisa zarginsu da laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Haka zalika kuma ana zargin gwamnatin Isra’ila da kisan kare dangi a gaban kotun kasa da kasa ta ICJ saboda ta’addancin da ta aikata a zirin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Harin Isra’ila a kan Iran ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zama dar-dar
An shiga yanayin zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya bayan wasu munana hare-hare da Isra’ila ta kaddamar a kan tashoshin Nukiliya da manyan sojojin Iran a ranar Alhamis.
Hukumomin Isra’ila dai sun tabbatar da kai harin inda suka ce ya kunshi daruruwan jirage kan abin da suka kira da kololuwar wurin hada makaman Nukiliya na Iran da kuma manyan sojojinta.
NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a KadunaDaga cikin manyan mutanen da ake zargin harin ya hallaka har da Manjo-Janar Hossein Salami, Shugaban Rundunar IRGC ta Iran da wasu manyan kwamandoji da manyan masana a tashar Nukiliyar.
Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta sanar da cewa jiragen yaki sama da 200 ne suka yi aikin kai hare-haren kuma sun kai su ne a muhimman wurare sama da 100 a Iran.
Sai dai jim kadan bayan labarin kai harin, Iran ta mayar da martani.
Kafofin yada labaran gwamnatin kasar sun rawaito cewa Iran ta harba jirage marasa matuka sama da 100 da suke hakon wurare daban-daban a cikin Isra’ila.
Kazalika, Shugaban addini na kasar, Ayatollah Ali Khomenei ya sha alwashin sai Isra’ila ta dandana kudarta.
Tuni rahotanni daga Isra’ila suka nuna yadda mutane suka shiga sayayya a kasuwanni ba ji ba gani suna adanawa saboda gudun abin da zai faru na martani.
Wasu hotuna da kamfanin dillancin labaran Faransa (AFP) ya wallafa sun nuna tituna a biranen Tel Aviv da Kudus sun dade.
Lamarin dai ya sa an soke tashi da saukar jirage zuwa kasashe da dama na yankin na Gabas ta Tsakiya.