IRGC : Iran a shirye take na tunkarar duk wani yanayi
Published: 12th, June 2025 GMT
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cikakken shirin Iran na tunkarar duk wani mataki na wuce gona da iri a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar barazanar daukar matakin soji kan kasar.
Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da rahotanni ke nuni da cewa, Amurka ta sanya ofisoshin jakadancinta da sansanonin sojinta da ke yammacin Asiya cikin shirin ko-ta-kwana saboda fargabar yiwuwar kai wa Iran hari.
“A wasu lokuta makiya suna yi mana barazana da daukar matakin soji, mun sha bayyanawa, kuma muna maimaitawa a yau, cewa mun shirya tsaf don fuskantar duk wani yanayi,” in ji shi.
“Muna da kwarewa, mun karfafa karfinmu tare da samar da dabaru a cikin tsare-tsarenmu.
Muna sa ido sosai kan sojojin abokan gaba kuma mun aiwatar da shirye-shiryenmu.” Inji shi.
Har ila yau babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya gargadi makiya game da duk wani gigi, ya kuma shawarce su da su yi la’akari da illolin da ayyukansu zasu haifar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)
Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin.
Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da tsaronsu, ta haka ne za su fara wasu tafiye- tafiye basu nan basu can, wanda idan ba sa’a aka yi ba, kusan ƙarshen ƙasar ke nan a matsayinta na tarayyar Nijeriya a lokacin. Duk wani ƙoƙarin da Abubbakar Tafawa Balewa ya yi na kasancewa ya zama kamar yadda Kwame Nkrumah na Ghana, wanda a zamaninsa kome ya ce daidai ne sai an bi ko amfani da shi, irin hakan ba zai iya haifar da ɗa mai ido ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp