Gwamnan Kebbi ya bai wa ’yan kasuwar katako tallafin ibtila’in gobara
Published: 10th, June 2025 GMT
Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya jajanta wa al’ummar kasuwar katako ta bayan kara da ke Birnin Kebbi bisa ibtila’in gobara da ta auka musu.
Mataimakin Gwamnan, Sanata Umar Abubakar Tafida ne ya wakilci gwamnan a yayin ziyarar jaje da ya kai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa.
A saurari sauyin da za mu yi wa ɓangaren man fetur a Nijeriya — Dangote NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen WayaA lokacin da ya zagaya domin duba irin ɓarnar da wutar ta yi a kasuwar, Mataimakin Gwamna ya yi kira da su mayar da lamarin ga Allah da kuma ɗaukar wannan ibtila’in a matsayin jarabawa daga gare Shi.
Haka kuma, ya miƙa wa ’yan kasuwar gudumawar Naira miliyan goma da gwamnan ya bayar a matsayin tallafi na farko domin rage musu raɗadin wannan ibtila’in.
Kazalika, ya bayyana cewar gwamnati za ta yi duk mai yiyuwa wajen taimaka wa ’yan kasuwar domin ci gaba da sana’ar su bayan an kammala ɗaukar bayanan da suka dace a kasuwa.
Shugaban ’yan kasuwar, Alhaji Bello Ɗan-Sambo, ya yi godiya ga gwamnan da mataimakinsa bisa ziyarar jaje da aka kai musu.
Haka kuma, ya yi godiya ga gwamnatin bisa gudunmawar Naira miliyan goma da ya bayar ga ’yan kasuwar da abin ya shafa.
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Lahadin da ta gabata ce gobara ta laƙume kasuwar katako da ke bayan kara a Jihar Kebbi.
Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 5:00 na Asuba bayan dawo da wutar lantarki, inda ta ƙone shaguna kimanin 30.
Aƙalla ’yan kasuwa tara ne gobarar ta shafa wacce ta laƙume dukiyar da ta kai kimanin Naira miliyan dari da casa’in.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Jihar Kebbi Kasuwar Katako yan kasuwar
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Na Maraba Da Karin ‘Yan Kasuwar Ketare Dake Son Gudanar Da Hada-hada Don Cimma Moriyar Juna
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp