Aminiya:
2025-09-18@00:48:41 GMT

An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato 

Published: 12th, June 2025 GMT

Aƙalla mutum 41 aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da aka kai wa jama’a daban-daban a Jihar Filato cikin mako guda da ya gabata.

Yankunan da aka kai wa hari sun haɗa da Bassa, Riyom, Bokkos da Ƙaramar Hukumar Mangu.

Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya

Hakazalika, an ruwaito cewa ɗaruruwan mutane sun rasa matsugunansu, an kuma ƙone gidaje da ba a san adadinsu ba.

Ɗaya daga cikin mafi munin hare-haren ya auku ne a ranar 8 ga watan Yuni, a ƙauyen Bauda da ke yankin Langai a Ƙaramar Hukumar Mangu.

’Yan bindiga sun shiga garin da sassafe, inda suka kashe mutum bakwai tare da ƙond gidaje 61, ciki har da cocin COCIN LCC.

A daren ranar, wasu ’yan bindiga sun sake kai hari garin Chinchim da ke yankin Mangu, inda suka kashe mutum takwas.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Mangu, Emmanuel Bala, ya tabbatar da aukuwar hare-haren.

“Mutane na cikin gidajensu lokacin da aka kai musu hari. An fi amfani da wuƙa wajen kashe su. Mutane takwas aka kashe a Chinchim. Kafin nan, mutane bakwai aka kashe a Bwai, kuma mun yi musu jana’iza a ranar Talata.”

Washegari, 9 ga watan Yuni, an sake kai hari a Gyenbwas da ke Langai, inda aka kashe mutum uku, an kuma ƙone gidaje sama da 90 ciki har da ginin JNI.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun sace abinci, shanu, katifu da sauran kayayyaki.

Sakataren Ƙungiyar Gan Allah Fulani Development Association of Nigeria (GAFDAN), Abubakar Garba, ya musanta zargin cewa Fulani ne suka kai hare-haren.

“Ba ma goyon bayan tashin hankali. Mambobinmu masu bin doka ne. Muna kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike don gano masu laifi,” in ji shi.

Wannan rikici ya daɗe yana faruwa tsakanin manoma da makiyaya a yankin, inda suke yawan kai wa juna hare-hare, lamarin da ke ƙara haifar da rashin yarda a tsakaninsu.

Wasu na ɗora laifi kan wasu ƙabilu, wanda hakan ke ƙara dagula lamarin.

A ranar 7 ga watan Yuni, an kashe mutum huɗu a ƙauyen Uwok-Ishe da ke Kekkek a Bassa.

Har ila yau, an sake kai hari Riyom, inda aka kashe wani yaro guda ɗaya, wani kuma ya jikkata.

Rahotanni sun ce an kashe wasu makiyaya biyu a Ancher, yayin da a Kwall aka kashe mutum uku, bayab kai wani hari cikin dare.

Duk da waɗannan hare-haren da suka faru a cikin ƙanƙanin lokaci, Gwamnatin Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa ba.

Har ila yau, babu wani martani daga kakakin rundunar ’yan sandan jihar ko rundunar Operation Safe Haven (OPSH), duk da ƙoƙarin da manema labarai suka yi na jin ta bakinsu.

Masana tsaro sun bayar da shawara kan yadda za a magance matsalar.

Tsohon jami’in ’yan sanda, SP Bulus Ajiji, ya ce: “Rashin haɗin kan al’umma da kuma rashin bayar da bayanai ga jami’an tsaro na daga cikin matsalolin. Wasu jama’a na kare miyagu kai-tsaye ko ba tare da sani ba.”

Masanin zaman lafiya kuma malami a jami’a, Joel Baba Alfa, ya bayar da shawarar matakan da za a ɗauka.

“Ya kamata gwamnati ta kai farmaki wajen da maharan ke ɓuya maimakon jiran suka kawo hari. Kuma a ƙirƙiro rundunar zaman lafiya ta al’umma wacce za ta ƙunshi dukkanin ɓangarorin da ke rikici da juna.”

Ya kuma ƙara da cewa: “Dole a riƙa bayyana gaskiya. Idan shanu sun mutu ko gonaki sun lalace, sai a sanar da jama’a. Haka kuma, kafofin watsa labarai su guji ɗaukar ɓangaranci kan addini ko ƙabila domin kaucewa tayar da rikici.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Makiyaya Zamab Lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.

Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.

Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.

“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.

Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.

Gwamnan ya kuma sake jaddada  cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.

Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza.
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato