HausaTv:
2025-09-18@00:43:01 GMT

Isra’ila ta hana ayarin motocin agaji na arewacin Afrika shiga Gaza

Published: 12th, June 2025 GMT

Ministan yakin Isra’ila, Israel Katz, ya umarci sojojin kasar da su hana ayarin motocin agaji na arewacin Afirka shiga yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

A cikin wata sanarwa ofishin Katz ya umarci sojojin Isra’ila da su hana “masu fafatuka daga Masar shiga yankin Zirin Gaza.

Katz bukaci “Hukumomin Masar dasu hana zuwan masu fafatukar a kan iyakar Masar da Isra’ila.

Ministan ya ya bayyana hakan a matsayin hadari ga jami’an tsaron Isra’ila na IDF.”

Wannan dai na zuwa ne bayan ayarin motoci 100 da ya kunshi dubban masu fafatuka daga kasashen Morocco, Aljeriya, Tunisia, Libya da Masar, suka yunkuri anniyar wayar da kan al’ummar duniya kan matsalar jin kai a Gaza, da neman kawo karshen yakin kisan kare dangi, da karya shingen da Isra’ila ke yi da kuma kai muhimman kayayyakin jin kai a Gaza.

Ayarin da ya kunshi kungiyoyin kwadago da masu fafutukar kare hakkin bil’adama da ‘yan wasa da lauyoyi da likitoci da ‘yan jarida da na kungiyoyin matasa da dai sauransu ana sa ran za su shiga Masar a yau Alhamis kafin isa mashigar Rafah da ke kan iyaka a kudancin zirin Gaza.

Kafin hakan dama sojojin Isra’ila sun kwace jirgin ruwan agaji na Madleen da ke kan hanyarsa ta zuwa Gaza domin kai tallafi ga al’ummar Zirin, bayan shafe sama da watanni ashirin na yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi.

An kama dukkan masu fafutukar na kasa da kasa su 12 da ke cikin jirgin, ciki har da mai fafutukar Sweden Greta Thunberg.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000

Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyya suke yi a Gaza ya doshi 65,000

Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin da yahudawan sahayoniyya suka kakaba wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza ya karu zuwa shahidai 64,871 da kuma jikkatan wasu 164,610 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.

Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar a zirin Gaza a ranar Lahadin da ta gabata, mutane 12,321 ne suka yi shahada yayin da wasu 52,569 suka samu raunuka tun bayan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake komawa yaki kan Falasdinawa a ranar 18 ga watan Maris.

A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Falasdinawa 68 ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu 68 da aka isa da su zuwa asibitocin Gaza.

Haka nan wasu Falasdinawa 10 sun yi shahada wasu 18 kuma suka jikkata da aka kai su asibitoci, lamarin da ya kawo adadin wadanda hare-haren ta’addancin ya rutsa da su a cikin bala’in neman tallafin abinci suka haura zuwa shahidai 2,494 da kuma wasu fiye da 18,135 da suka samu raunuka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza
  • Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
  • Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000
  • Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa