Saudiyya za ta fara bayar da bizar Umara
Published: 11th, June 2025 GMT
Bayan kammala aikin Hajjin bana, Saudiyya za ta fara bayar da bizar umara daga gobe Laraba.
Kazalika mahukuntan ƙasar sun ce dakatarwar shiga birnin Makkah ba tare da takardar izini ba zai ƙare daga ranar Larabar 11 ga watan Yunin 2025.
Dalilin da Nijeriya ke fuskantar tsaiko wajen karɓar rancen $5bn daga Saudiyya Gwamnan Kebbi ya bai wa ’yan kasuwar katako tallafin ibtila’in gobaraMa’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ta ce za ta fara karɓar sabbin baƙi masu shigar ƙasar da bizar Umarah daga gobe Laraba, 11 ga watan Yuni.
Sanarwar na zuwa bayan kammala aikin Hajjin bana wanda kimanin mutum miliyan 1.6 daga faɗin duniya suka halarta.
Saudiyya takan dakatar da bayar da bizar umara makonni gabanin aikin Hajji domin bai wa mahukunta damar jiɓintar shirye-shiryen ibadar da ake gudanarwa duk shekara.
Wannan dakatarwar tana bai wa mahukunta damar mayar da hankali kan kula da hidimar mahajjata musamman a fannin tsaro, lafiya da sauran buƙatu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan.
An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa.
Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai.
An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni.
Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi.
Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp