HausaTv:
2025-11-03@00:54:21 GMT

 Mutane 2 Sun Yi Shahada A Wani Harin HKI A Kudancin Kasar Lebanon

Published: 10th, June 2025 GMT

Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wani hari a garin “Aytas-sha’ab’ dake kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane biyu.

Kafafen watsa labarun Lebanon sun ambaci cewa, mutanen biyu da su ka yi shahada sun hada da wani makiyayi da dansa da suke kiwon dabbobinsu a burtalin dake kan iyaka da Falasdinu dake karkashin mamaya.

 A jiya Litinin ma dai wani jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniyar, ya kai hari a garin Nabadhiyyah. Har ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan ko harin na jiya ya yi sanadiyyar shahadar wasu ko jikkata. Sai dai kuma gobara ta tashi a cikin motar da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa harin na jiya.

Daga lokacin da HKI ta kai wa kasar Lebanon hari a ranar 8 ga watan Oktoba 2023, mutane da dama sun rasa rayukansu da adadinsu ya kai 4000, sai kuma wasu 17,000 da su ka jikkata. Har ila yau, wasu mutanen Lebanon da sun kai miliyan daya da 400,000 sun yi hijira.

Amma daga lokacin da aka tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Nuwamba HKI ta keta yarjejeniyar sau 3000,  ta kuma kashe mutane 209 da jikkata 504,kamar yadda kamfanin dillancin labarun Anatoli ya ambata.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A
  • Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar