Tinubu Ya Ceto Nijeriya Daga Faɗawa Matsin Tattalin Arziƙi – Gwamna Namadi
Published: 11th, June 2025 GMT
A cewarsa, shuwagabancin Tinubu ya gina tubalin ci gaba mai ɗorewa ta hanyar yanke hukunci masu wahala amma masu amfani.
Dangane da sauyin jam’iyyun siyasa da ke faruwa, Namadi ya ce yawaitar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC alama ce da ke nuna yadda jama’a ke ƙara amincewa da shugabancin Tinubu da kuma burin da yake shi ga ƙasar nan.
Ya ce masu barin jam’iyyunsu suna haka ne domin suna ganin makoma mai kyau a ƙarƙashin jagorancinsa.
Har ila yau, Namadi ya bayyana cewa ziyarar aikin da ya kai Indiya kwanan nan ta samar da muhimman yarjejeniyoyi da masu saka jari da ƙwararru don bunƙasa harkar noma a Jihar Jigawa.
Ya ce an cimma matsaya a fannoni irin su kiwon shanu, kiwon kaji da samar da ingantattun iri, wanda zai ƙara samar da ayyukan yi, tsaro na abinci, da kuma ɗora Jigawa zuwa cibiyar noma ta ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gwamna Namadi Jigawa Tattalin Arziƙi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Ƙwaya A Kano
Mambobin kwamitin sun haɗa da:
1. Barr. Aminu Hussain – Shugaba
2. Barr. Hamza Haladu – Mamba
3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba
4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba
5. Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.) – Mamba
6. 6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba
7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya
Yayin da yake sanar da kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar damuwarsa game da zargin da ke kan jami’in gwamnati, tare da jaddada aniyarsa ta yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da duk wasu munanan ɗabi’un da ba su dace ba a fadin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp