Ƙungiyar G-5 Ta Ceto Nijeriya Daga Faɗa Wa Rikici — Wike
Published: 10th, June 2025 GMT
“Mun bi tsarin mulki kuma mun ƙi rashin adalci. Da PDP ta yi haka, ba za ta fuskanci wannan matsala ba.”
Taron ya haɗa da tsoffin gwamnonin jihohi Samuel Ortom (Benue) da Okezie Ikpeazu (Abia), da sauran shugabannin jam’iyyar.
Wike ya soki shugabannin PDP saboda sanya son rai fiye da haɗin kan jam’iyyar.
Ya ce jam’iyyar sai ta koma tubalinta na asali don samun ci gaba.
“Wasu shugabanni suna karkatar da dokoki don amfanin kansu,” in ji Wike, yana ambaton yadda gwamnan Taraba ya tsaya takarar gwamna ba tare da ya yi murabus a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ba.
“Dole ne a daina wannan.”
Tsohon Gwamna Ortom ya yarda da maganar Wike, ya amince cewa PDP ta yi manyan kurakurai.
“Muna buƙatar taimakon Allah don gyara jam’iyyar,” in ji shi.
Ƙungiyar G-5 wadda ta haɗa da Wike, Ortom, Ikpeazu, Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), da Seyi Makinde (Oyo), sun yi adawa da takarar Atiku Abubakar a zaɓen 2023, wanda suka ce hakan ya saɓa wa dokar tsarin karba-karba.
Adawar ta jefa jam’iyyar PDP cikin matsalolin wanda hakan ya kai ta ga faɗuwa zaɓen 2023.
Yanzu, Wike yana aiki a ƙarƙashin Shugaba Tinubu amma har yanzu yana iƙirarin shi memba ne na jam’iyyar PDP, wanda ke ƙara dagula wa jam’iyyar lissafi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma
Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin karshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a wadannan kasashe.
“Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntubar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun karin umarni.”
Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da fada tsakanin Isra’ila da Iran, tare da bukatar bangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare hakkin dan Adam na duniya, kuma su bai wa rayuwar fararen hula muhimmanci.
Ma’aikatar ta jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan hanyoyin warware rikici ta hanyar lumana da kuma tallafa wa zaman lafiya a yankuna da duniya baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp