Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3
Published: 11th, June 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba, ta dakatar da shugabar Ƙaramar Hukumar Bekwara, Hon. Theresa Ushie, na tsawon wata uku, domin a gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake mata.
An ce kimanin wakilan ƙaramar hukumar 10 daga cikin 11 ne suka yi ƙarar shugabar, inda tara daga cikinsu suka rattaba hannu suna goyon bayan a dakatar da ita.
Ɗaya daga cikin wakilan ne kawai bai yarda ba.
Ana zargin Hon. Ushie da amfani da kuɗin Ƙaramar Hukumar ba tare da shawarar majalisar jihar ba, tare da yin wasu muhimman ayyuka ba tare da tuntuɓar ’yan majalisar ba.
Mai magana da yawun Gwamnan jihar, Nsa Gill, ya bayyana cewa an dakatar da shugabar ne domin a samu damar yin cikakken bincike cikin kwanciyar hankali.
Shugaban majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Elvert Ayambem, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bisa sashe na 14(3) na dokokin ƙananan hukumomin jihar da aka kafa tun 2005.
A halin yanzu, majalisar ta amince da naɗa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Egbung Odama, a matsayin shugaban riƙo har zuwa lokacin da binciken zai kammala cikin wata uku masu zuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dakatarwa Shugabar Ƙarama
এছাড়াও পড়ুন:
An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
’Yan sanda a jihar Legas sun kama wani tsohon fursuna tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a jerin laifukan fashi da yankan aljihu a jihar kwana biyar da fitowa daga kurkuku.
Tsohon fursunan mai shekaru 25 da haihuwa, Segun Kolawole, an kama shi ne bayan kwana biyar da aka sako shi daga cibiyar gyaran hali ta Kirikiri, a jihar Legas.
Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano SpalletiSauran wadanda aka kama tare da shi sun haɗa da Sodiq Isa mai shekaru 27 da Adekanmbi Ganiu mai shekaru 21.
Rahotanni sun nuna cewa an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifukan yankan aljihun mutane da sauran laifukan sata a sassa daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da cafke Kolawole, inda ta ce an kama shi da misalin ƙarfe 8 na safiyar Talata a kasuwar Oshodi, bayan jami’ai sun lura da motsinsa da ya zama abin zargi.
Adebisi ta ce an same shi da tsabar kuɗi ₦80,000 da wayar Infinix Note 40 Pro, waɗanda aka gano daga wani fashi da ya aikata a Opebi, inda ake zargin ya saci ₦200,000 da wayar daga hannun wani ɗan kasuwa da ke barci.
“Bincike ya ƙara tabbatar da cewa ya riga ya sayi sabbin kaya da takalma da wani ɓangare na kuɗin da ya sata, waɗanda suma aka kwato su daga hannunsa,” in ji ta.
Haka kuma, a wani samame daban da aka gudanar da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Juma’a, jami’an RRS sun kama Sodiq Isa da Adekanmbi Ganiu bisa zargin yunkurin satar wayoyin hannu daga hannun fasinjoji a sassa daban-daban na Legas.