Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabom Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu
Published: 12th, June 2025 GMT
Ministan tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar sun yi gwajin wani makami mai linzami wanda yake iya daukar abubuwan fashewa hart un biyu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Amir Nasirzade yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa . wannan gwajin sako ne ga gwamnatin Amurka da kawayenta.
Yace iran tana cikin fushi kan abinda yake faruwa a Gaza don haka duk wata dama da ta samu zata maida martanin da ya dace. Ministan ya bayyana haka ne a jiya Laraba bayan taron Majalisar ministoci tare da shugaban kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar
Kasar Sin ta bullo da wani shirin bayar da tallafin kula da yara a fadin kasar wanda zai fara aiki daga shekarar 2025, a wani bangare na kokarin tallafa wa iyalai da kuma karfafa yawan haihuwa.
Shirin zai bai wa iyalai tallafin yuan 3,600, kimanin dalar Amurka 503, a kowace shekara a kan kowane yaro da bai kai shekaru uku da haihuwa ba.
Za a kebe tallafin daga cire harajin kudin shiga kuma ba za a kidaya shi a matsayin kudin shiga na iyalai ko na mutum daya ba a yayin da ake tantance masu karbar taimakon, inda abun zai zama kamar dai irin na wadanda ke karbar alawus na cin abinci ko kuma wadanda ke rayuwa cikin matsananciyar wahala. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp