Iran ta Yi Gargadin Cewa Zata Fice Daga Yarjeniyar NPT Idan Hukumar IAEA Ta Tir Da Ita
Published: 12th, June 2025 GMT
JMI ta bayyana cewa zata yi amafani da hakkinta wanda doka ya bata na ficewa daga yarjeniyar NPT don sake farfado da takunkuman tattalin arziki na MDD a kan kasar.
Jakadan kasar Iran a MDD, Amir Saeid Iravani ne ya bayyana haka a jiya Laraba.
Kamfanin dillanbcin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a wata wasika da ya rubutawa kwamitin tsaro na MDD a jiya.
Kasashen Turai guda Uku jamusa Farana da Burtania suna son su yi amfani da damar da ake kira snap back don sake farfado da takunkuman MDD a kan kasar na yarjeniyar JCPOA.
Ya kammala da cewa yarjeniyar JCPOA bata da amfanmi bayan da suka kauracewa yin aiki da ita na shekaru.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA