Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Cimma Daidaito Da Sin Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya
Published: 13th, June 2025 GMT
Zuzzurfar tattaunawa da ta wakana tsakanin tsagin Sin da na Amurka a birnin Landan, ta sa masu bayyana ra’ayoyin jin karfin gwiwa game da makomar shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka.
Kuri’un jin ra’ayin jama’a na kafar CGTN ta kasar Sin, sun nuna yadda masu bayyana ra’ayoyi suka amince cewa, shawarwari sun nuna kyakkyawan fata game da aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, tare da sassauta sabani a batutuwan tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu.
Yayin kuri’un jin ra’ayoyin, masu bayyana mahanga sun goyi bayan matsayar Sin, inda kaso 87.1 bisa dari suka amince cewa ba wani batu na wa ya yi nasara, ko wanda ya yi hasara a batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu.
Kaso 85.2 bisa dari na ganin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ba kawai zai kyautata ci gabansu ba ne, har ma zai samar da wani muhimmin tabbaci ga daidaito, da bunkasar tsarin gudanar da ayyukan masana’antu na duniya. Yayin da kaso 87.1 bisa dari ke ganin managarcin tsari, da daidaiton ci gaban alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ba kadai zai amfani al’ummunsu ba ne, har ma zai samar da muhimmiyar gudummawa ga bunkasar tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tattalin arziki da cinikayya tsakanin
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.
Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.
Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp