An Bude Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afirka A Changsha
Published: 12th, June 2025 GMT
A yau Alhamis ne aka bude bikin baje kolin hada-hadar tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu a birnin Changsha fadar mulkin lardin Hunan, taron dake kara jaddada himmar kasar Sin ta fuskar karfafa alaka da nahiyar Afirka, nahiyar dake da mafiya yawan kasashe masu tasowa a duniya baki daya.
Kusan kamfanonin Sin da na kasashen Afirka 4,700, da sama da mahalarta 30,000 ne za su halarci bikin na kwanaki hudu, wanda aka yiwa taken “Sin da Afirka: Tunkarar zamanantarwa tare.” Rahotanni daga mashirya bikin na cewa, kwarya-kwaryar darajar ayyukan hadin gwiwa da aka amincewa sun haura dalar Amurka biliyan 11.
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin bude baje kolin, inda kuma ya yi amannar cewa taron zai samar da karin damammaki ga hadin gwiwar Sin da Afirka, tare da haifar da kyakkyawan sakamako.
Wang Yi, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya kara da cewa, duk irin sauyin da aka samu a fannin cudanyar sassan kasa da kasa, Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da nahiyar Afirka, za ta samar da kakkarfan tallafi ga ayyukan zamanantar da nahiyar, da kasancewa kawa ta gari, kuma sahihiyar ‘yar uwa ga Afirka kan hanyar nahiyar ta samun ci gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo.
Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida.
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDPMai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada.
Sai dai a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar da yammacin ranar Juma’a, kakakinta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar ba za ta dakatar da shirin gudanar da taron ba.
Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin tauye haƙƙin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ologunagba, ya ce hukuncin ba zai hana PDP ci gaba da shirye-shiryenta na zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa ba.
Ya yi nuni da cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa jam’iyyu na da ’yancin tafiyar da harkokinsu na cikin gida.
“PDP na kira ga mambobinta da shugabanni a faɗin ƙasar nan da su kuma ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar mai bin doka ce, kuma ta umarci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun.