HausaTv:
2025-11-03@04:03:11 GMT

Iran ta caccaki kudurin IAEA wanda ta ce yana cike da siyasa

Published: 12th, June 2025 GMT

Iran ta yi Allah-wadai da wani kuduri da ta danganta da na siyasa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta dauka, tana mai cewa ba shi da tushe na fasaha ko doka.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) da ma’aikatar harkokin wajen kasar sun fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Alhamis bayan da majalisar gwamnonin hukumar ta IAEA suka amince da wani kuduri da ke zargin Iran da rashin cika alkawuran da ta dauka na nukiliya.

Kuri’u 19 ne suka amince da kudurin wanda Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus suka tsara.

Kasashen Rasha, China da Burkina Faso sun kada kuri’ar kin amincewa da shi, Yayin da kasashen Afirka ta Kudu, Indiya, Pakistan, Masar, Indonesia da Brazil suka ce su kam ba ruwan su.

Sanarwar da Iran ta fitar dangane da wannan kudiri ta ce, Jamhuriyar Musulunci ba ta da wani zabi face mayar da martani ga wannan kudiri na siyasa.”

Sanarwar ta ce, Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, ya ba da umarnin gina sabuwar cibiyar tace uranium a wani wuri mai aminci.

Sabuwar cibiyar za ta kunshi sabbin na’urorin tace uranium na zamani inji sanarwar.

A cikin sanarwar, Tehran ta yi tir da kudirin na “siyasa da son zuciya” na IAEA  Wanda Amurka da manyan kasashen Turai uku – Faransa, Jamus da Birtaniya suka tsara.

Iran ta kuma yi tir da shirun da Amurka da kawayenta na Turai suka yi wajen tinkarar yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kin mutunta yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Iran da Amurka suka tabbatar da sake ganawa a karo na shida a ranar Lahadi mai zuwa game da shirin nukiliyar Iran wanda a’a gudanar a birnin Muscat a shiga stakanin kasar Oman.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Maganin Nankarwa (3)

Yawan shafa man kade a wurin ma yana rage ta sosai.

Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zarar sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ne babu Kemikal a cikinsa don haka yana daukar lokaci kafin a ga canji kamar, sati biyu idan ba ki ga canji ba sai ki dauki wani kuma.

Allah shi ne masani. Allah yasa mu dace.

Ga hanyoyi guda 5 da za’a iya magance su a saukake ba tare da amfani da mayuka masu illlata fata ba

Hanya ta 1: Dankalin Hausa

Dankali yana dauke da sinadarin sitaci da yake lausasa fata da kuma sinadarin da yake hana fata lalacewa wato antiodidant. Haka kuma dankali yana dauke da sinadarin bitamin C, potassium, thiamin, riboflabin, iron, zinc da sauran su.

Yanda ake amfani da shi:

A yanka Dankali sannan a shafa a hankali a kan Nankarwar. Sai a bar shi na tsawon mintuna 15 zuwa 20, sannan a wanke da ruwan dumi. A maimaita haka a kullum

Hanya ta 2: Alo bera

Ruwan da ke cikin Alo bera yana dauke da sinadarin Collagen wanda aka san shi da gyara fatar da ta lalace da kuma kara laushin ta, kyanta da kuma yarintar ta.

Yanda ake amfani da shi:

A karya itacen Alo bera guda sai a shafa ruwan a kan Nankarwa. A bar shi tsawon awa 2 zuwa uku sai a wanke da ruwa. A maimata hakan a kullum har sai an samu sakamako mai kyau.

Hanya ta 3: Man kadanya da koko Bota

Hadin man kadanya da koko Bota yana dauke da sinadarin bitamin E da kuma sinadaran da ke hana fata lalacewa

Yadda ake amfani da shi

Za’a samu Koko Bota karamin cokali 2, da man kadanya shima karamin cokali 2, sai sinadarin Bitamin E karamin cokali 1. Za’a narka man kadanya da kuma man koko Bota sai a kara bitamin E din a ciki a gauraya. Za’a dura gaba daya a cikin mazubi a ajiye ana shafawa a kan Nankarwar kullum.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa November 2, 2025 Manyan Labarai Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka November 2, 2025 Labarai Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a Yobe
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Maganin Nankarwa (3)
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi
  • Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare