Shugabannin Sin Da Kongo (Brazaville) Sun Aike Da Wasikun Taya Murna Ga Taron Ministocin Kula Da Aiwatar Da Sakamakon Taron FOCAC
Published: 11th, June 2025 GMT
Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Kongo Brazaville Denis Sassou Nguesso, sun aike da wasiku na taya murna ga taron ministocin kula da harkokin da suka shafi aiwatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC, inda suka taya murnar bude taron.
Cikin sakonsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, yanayin kasa da kasa ya cika da sauye-sauye da hargitsi. Kuma kasar Sin ta dage wajen samar da sabbin damammaki ga duniya tare da sabbin nasarorin da aka samu na zamanantarwa iri ta kasar Sin, da samar da sabon kuzari ga kawayen kasashe masu tasowa na duniya kamar kasashen Afirka ta hanyar shiga a dama da su a babbar kasuwarta. Kasar Sin tana son yin shawarwari da rattaba hannu kan yarjejeniyar huldar abokantaka ta raya tattalin arziki tare, da aiwatar da manufar soke haraji da kaso 100 bisa 100 kan wasu hajojin dake shiga kasar daga kasashen Afirka guda 53 masu huldar diplomasiyya da ita, sa’an nan kuma za ta samar da karin sauki ga kasashe masu karamin karfi na Afirka don fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin.
Manchester City Ta Kammala Daukar Rayan Cherki Daga Lyon Nan Ba Da Jimawa Ba Harkar Man Fetur Za Ta Sauya A Nijeriya – DangoteXi Jinping ya yi nuni da cewa, yana fatan kasashen Sin da Afirka za su ci gaba da sa kaimi ga aiwatar da sakamakon taron kolin, da tsara yadda za a bunkasa dandalin a nan gaba, da yin hadin gwiwa don gina al’umma mai makoma ta bai-daya ta Sin da Afirka a sabon zamani, da ba da gudummawar karfin Sin da Afirka wajen gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai-daya ga daukacin bil’adama.
A cikin wasikar taya murnar, Sassou ya bayyana cewa, tun bayan taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a nan birnin Beijing, an samu sakamako mai kyau na hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin. Kana ya ce, zai ba da himma tare da shugaba Xi Jinping ba tare da kakkautawa ba, don sa kaimi ga samun babban ci gaba a fannin gina al’umma mai makomar bai-daya ga Afirka da Sin, da kuma kara kyautata jin dadin jama’ar bangarorin biyu. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a.
Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu.
Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga mutane da birane.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da wata ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta Janar na birnin Dubai inda suka tattauna batutuwan haɗin gwiwa a fannin kirkirar makamashin sharar gida da kula da sharar gida ta zamani, da kuma tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
A ganawar, duk Bangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin jihar Kaduna zuwa tattalin arzikin mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Jihar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun ƙasashen duniya wajen yin haɗin kai, ƙirƙira, da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa da ci gaban kowa da kowa a fadin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA