Burtaniya Ta Kakabawa Ministocin HKI Guda 2 Takunkuman Tattalin Arziki
Published: 11th, June 2025 GMT
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bada sanarwan kakabawa ministocin HKI guda biyu takunkuman tattalin arziki saboda ra’yinsu na wuce gona da Iri wanda zai bata duk wani shirin da kasashen duniya suke da shin a tabbatar da zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kira-kirayen ministocin na kara mamaya da kuma korar falasdina daga yankin yamma da kogin Jordan ne yasa burtaniya ta nuki wannan batakin.
Bezalel Smotrich dai , wanda shi ne ministan kudi na HKI ya ce HKI zama kara mamayar yankin yamma da kogin Jordan, kafin zaben shekara ta 2026, sannan ya rantse kan cewa za’a share falasdinawa a gaza, kuma zasu wargaza kungiyar Hamas a cikin yan watanni masu zuwa.
Sannan Itamar Ben-Gvir kuma wanda ya kasance ministan harkokin yakin kasar ya bukaci a kara ginawa gidaje sannan a fadada kai hare-hare a kan falasdinawa ta yadda nan gab aba wanda zai sake maganar warware rikicin gabas ta tsakiya ta hanyar kafa kasashe biyu.
Takunkuman tattalin arziki zai iya tada jijiyoyin wuya a tsakanin kasashen biyu amma kuma ba zasu hana HKI yin abinda ta ga dama ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Watse A Taron EU Da China Saboda Ricikin Kasuwanci Da Siyasa Tsakaninsu
An takaita taro tsakanin kasashen turai da China a birnin Beijin zuwa ranar Alhamis kadai bayan da bangarorin biyu sun sami sabani a tsakaninsu kan al-amuran kasuwanci.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron har na tsawon kwanaki uku amma kwotsom sai kasar China ta bukaci a takaita taron zuwa jiya Alhamis kadai.
A nata bangaren shugaban tarayyar ta turai Ursula von der Leyen ta bayyana cewa, kasat China ce kadai take amfani da tsarinn kasuwancin da ke tsakanin bangarorin biyu, ta bada misali da cewa bambancin ribar da china take samu a cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai Euro biliyon 305.8 ko dalar Amurka biliyon 360 a shekarar da ta gabata kadai. Sannan harkokin kasuwanci a tsakanin Eu da China yana karuwa kamar yadda bambanci da rashin daidaito yake karuwa. Don haka tace dole ne a sauya tsarin. Amma gwamnatin kasar China ta ce rashin daidaito a harkokin kasuwanci tsakanin bangarorin biyu ba daga kasar China ya taso ba, saboda kasashen Eu suna harkokinnwasuwanci da kasashen duniya da dama. Shugaban kasar China Xi Jinoing ya bukaci kungiyar EU ta gyara harkokin kasuwancinta da kanta.