An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato
Published: 12th, June 2025 GMT
Aƙalla mutum huɗu ciki har da jaririn wata tara aka kashe a wani hari da aka kai ƙauyen Nkiendowro da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato.
Mutanen da suka rasu sun haɗa da mata biyu da namiji ɗaya, wanda aka ce suna aikin jigilar kwashe tumatir daga ƙauyen zuwa kasuwar Farin-Gada da ke Jos lokacin da aka kai musu hari.
Wasu mutum biyu kuma sun jikkata a harin, wanda yanzu haka suna karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
Shugaban tsaron al’ummar Miango, Josiah Zongo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an ajiye gawarwakin, yayin da waɗanda suka jikkata ke karɓar kulawa.
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa ba kan harin.
A wani lamari makamancin haka, an kai hari ƙauyen Murish da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a daren ranar Laraba, amma matasa da mazauna ƙauyen sun yi nasarar kare kansu daga maharan.
Wani matashi daga ƙauyen ya bayyana cewa maharan sun shigo suna harbi, amma mutanen ƙauyen sun kare kansu.
Shohotden Mathias Ibrahim, Daraktan Al’adu na ƙungiyar Mwaghavul Development Association kuma shugaban sansanin ‘yan gudun hijira a Mangu, ya roƙi al’umma da su kwantar da hankali su ci gaba da harkokinsu cikin lumana.
Ƙananan hukumomin Mangu da Bassa sun fuskanci hare-hare da dama a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin al’umma game da tsaro a Jihar Filato.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hari
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.
Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa.
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Ukuwannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai.
Domin sauke shirin, latsa nan