EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna
Published: 12th, June 2025 GMT
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama mutane 11 da ake zargi da aikata damfara a Intanet a Jihar Kaduna.
Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a unguwannin Mahuta da Barnawa bayan samun sahihan bayanai game da ayyukansu na yaudara ta yanar gizo.
A lokacin da aka kama su, EFCC ta ƙwace wasu kayayyaki daga hannunsu da suka haɗa da mota ƙirar Mercedes Benz C300 mai launin baƙi, wayoyi 14, kwamfutoci guda biyu, iPad, na’urorin mifi guda biyu, lasifikar JBL guda ɗaya, da kuma lasifikar zealot guda ɗaya.
EFCC ta ce za a gurfanar da su gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Damfara
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq.
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoSun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi.
A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Saudiyya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya bayar da cikakken goyon baya wajen ganin an saki waɗanda aka kama.
Bincike ya gano cewa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi ne a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, suka ƙwayoyin a jakunkuna waɗanda aka kama.
Mutanen uku da aka kama, sun tashi a jirgin Ethiopian Airlines a ranar 6 ga watan Agusta don yin Umara, amma aka kama su a Saudiyya.
Binciken NDLEA ya kai ga kama wani shugaban masu safarar miyagun ƙwayoyin, mai shekaru 55, Mohammed Ali Abubakar (wanda aka fi sani da Bello Karama).
Hakazalika, hukumar ta kama wasu mutum uku ciki har da ma’aikatan jirgi.
Mutanen da aka kama su ne suka shirya safarar ƙwayoyin a jakunkunan mutane da aka kama a Saudiyya.
NDLEA ta gabatar da shaidun da suka tabbatar da cewa mutanen da aka kama a Saudiyya ba su da laifi.
Sakamakon haka, hukumomin Saudiyya suka sako ɗaya daga cikinsu a ranar 14 ga watan Satumba, sannan suka sako sauran biyun a ranar 15 ga watan Satumba.
Babafemi, ya ce Marwa ya gode wa hukumomin Saudiyya saboda mutunta yarjejeniyar haɗin kai tsakaninsu da Najeriya.
Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu da sauran manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Shari’a, Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Ministan Sufurin Jiragen Sama, da Mai Bai Wa Shugaba Shawara Kan Harkar Tsaro, saboda gudummuwarsu.
Ya ƙara da cewa wannan lamari ya nuna cewa Najeriya tana tsayawa wajen kare ‘yan ƙasarta a ƙasashen waje kuma ba za ta yadda wani ɗan Najeriya ya sha wahala saboda laifin da bai aikata ba.