Ranar Dimokuraɗiyya: Gwaman Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
Published: 12th, June 2025 GMT
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri.
Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai.
“Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara) da kuma shawarwarin kwamitin bayar da shawara kan jinƙai, don haka na yi afuwa ga fursunoni 66 da ke babbar cibiyar gyaran hali da ke nan Maiduguri,” in ji Zulum.
Ya kuma ƙara da cewa “Na kuma mayar da hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai-da-rai tare da rage wa wasu fursunoni hukuncin zaman gidan yari a wani ɓangare na bukukuwan murnar zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya ta bana.”
“Bayan afuwar, Gwamna Zulum ya yi wani gagarumin tallafi ta hanyar ba da gudummawar tsabar kuɗi Naira dubu 20 ga kowanne fursunoni 1,280 da ke cikin wannan gidan gyaran.”
Don ci gaba da gudanar da bukukuwan ranar dimokraɗiyya a cibiyar, ya kuma sanar da bayar da gudummawar buhunan shinkafa 300, galan 50 na man girki, da shanu guda 5.
Da yake mayar da jawabi Kwanturolan gidan gyaran hali na jihar Borno, Ibrahim Bawa ya yaba da ziyarar da Gwamnan ya kai wanda ya ce ba a taɓa yin irinsa ba.
“Wannan shi ne irinsa na farko,” in ji shi.
Yana mai cewa, babu wani gwamnan da ya gabata da ya ziyarci wurin domin yin murna ga fursunonin, musamman waɗanda suka yi sa’ar shaƙar iskar ’yanci.
Bawa ya kuma tuno da irin karamcin da Gwamnan ya yi a baya da suka haɗa da kyaututtukan buhunan shinkafa 100, galan-gadan na man girki 25, da bijimai 10 a lokacin bikin Sallah na Eid-el-Kabir na baya, wanda ya ce duk fursunoni da ma’aikata sun ji daɗin su.
Mista Gambo Samuel, wanda aka fi sani da Sarkin Gida, kuma shugaban fursunonin, ya nuna matuƙar godiya ga Gwamna Zulum dangane da wannan alfarma da ya musu na afuwar da kuma kayan abincin da ya kawo musu tallafinsa.
Ya kuma yaba wa ƙoƙarin Gwamnan na kawo sauyi a faɗin jihar, wanda ya lura akai-akai ana jin labarin sa daga sabbin fursunonin da ke shigowa wannan cibiyar lokaci zuwa lokaci.
Baya ga ziyarar da ya kai gidan gyaran halin, Gwamna Zulum ya kuma ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da dama na tunawa da ranar dimokuraɗiyya a cikin birnin Maiduguri da suka shafi hanyoyin mota, ruwan sha, cibiyoyin kiwon lafiya da makamantansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ranar Dimokuraɗiyya Gwamna Zulum
এছাড়াও পড়ুন:
ICPC Ta Gurfanar Da Ma’aikacin Kotu Bisa Badakalar Naira Miliyan 9.2
Abdulazeez pleaded not guilty to the two-count charge. Abdulazeez ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da su biyu.
Bayan rokon da ta yi, lauyan ICPC, Hamza Sani, ya bukaci kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2025, domin masu gabatar da kara su gabatar da shaidu.
Sai dai daga baya kotun ta ba da ranar sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yunin 2025 domin sauraron karar.
Lauyan wanda ake tuhuma ya nemi a ba shi belin, wanda ICPC ba ta yi adawa da shi ba.
Mai shari’a Iheabunke ya bayar da belinta a kan kudi naira miliyan 10, tare da mutane biyu da za su tsaya mata.
Ya ce dole ne wadanda ake kara su mallaki kadarorin da ke karkashin ikon kotun, sannan su mika takardun mallakar asali ga magatakardar kotun don tantancewa, sannan wanda ake kara ya sanar da kotu a hukumance kafin tafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp