Nijeriya Ta Fuskanci Cikas Wajen Karɓo Rancen Dala Biliyan 5 Daga Saudiyya
Published: 11th, June 2025 GMT
Amma har zuwa yanzu, babu cikakken bayani daga Gwamnatin Tarayya.
A watan Mayun 2025 ne Tinubu ya miƙa buƙatar samun amincewar majalisa domin karɓar rancen Dala biliyan 21 daga ƙasashen waje, ciki har da Dala biliyan biyar daga Aramco.
Rahoton Reuters bai bayyana sunayen bankunan da za su taimaka ba, amma majiyoyi sun ce ɗaya daga cikin bankunan na nahiyar Afrika ne, sauran kuma daga Gabas ta Tsakiya.
Idan aka cimma yarjejeniyar, wannan zai zama mafi girma daga cikin bashin da Nijeriya ta taɓa karɓa a irin wannan hanya daga Saudiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya Rance Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons) ta samu a gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) 2025, inda ya ce yana sa ran karɓar kofin daga hannunsu a Abuja.
A cikin wata hira ta bidiyo da aka yi da shugaban ƙasa jim kaɗan bayan wasan, tare da kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da wasu ‘yan wasan da jami’an tawagar, Tinubu ya taya su murna bisa lashe kofin karo na 10. Ya ce wannan nasara wata hanya ce da ke ɗaukaka darajar Nijeriya a idon duniya.
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC Na Ƙasa, Farfesa Yilwatda“Ina alfahari da ku, Nijeriya gaba ɗaya na alfahari da ku. Kun ɗaga martabar ƙasarmu, ku abin koyi ne a zamanin ku. Ina mika godiya ta musamman ga masu horar da tawagar,” in ji Tinubu, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar. Shugaban ya kuma miƙa saƙon ban girma ga Rasheedat Ajibade da ta samu lambar gwarzon ‘yar wasa a gasar.
Yayin da yake zantawa da tawagar, Tinubu ya yi addu’ar dawowar su lafiya zuwa gida, yana cewa: “Ina fatan zaku iso lafiya, Allah ya saka muku da alheri.” A madadin tawagar, Rasheedat ta gode wa shugaban ƙasa bisa amincewa da biyan cikakken alawus na ‘yan wasan, tana mai tabbatar masa da cewa tawagar za ta ba da dukkan ƙoƙarinta wajen kawo kofin WAFCON zuwa Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp