DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya
Published: 11th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso.
Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa.
A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka daga jami’an lafiya.
Sai dai ’yan Najeriya da dama sun dade suna kokawa da yadda a cewarsu wasu jami’an kiwon lafiya kan nuna halin ko-in-kula, a wasu lokutan ma da sakaci, wanda kan kai rasa rayuka. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai zube komai a faifai don gano sahihancin wannan zargi da ’yan Najeriya suke yi da kuma, idan zargin ya tabbata, yadda aikin jami’an lafiya ya yi hannun riga da abin da aka karantar da su.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jami an kiwon lafiya Marasa Lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.
Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.
Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp