Hamas : Ziyarar ministan Isra’ila Ben-Gvir a masallacin al-Aqsa kan iya tayar da yakin addini
Published: 12th, June 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da kutsawa cikin masallacin al-Aqsa da ministan Isra’ila Itamar Ben-Gvir ya yi a baya bayan nan, tana mai cewa tana da nufin tayar da “yakin addini” a wannan wuri mai tsarki.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce “Kutsen da Itamar Ben-Gvir, ya yi a cikin masallacin Al-Aqsa mai alfarma, da kuma ziyarar tsokanar da ya kai a harabar masallacin… rashin mutunta ra’ayin musulmi da kuma keta alfarma da matsayin masallacin Al-Aqsa a duniyar Musulunci.
Kungiyar ta jaddada cewa wannan wulakanci da aka yi yana nuna ” girman kai na wannan gwamnati mai tsattsauran ra’ayi da kuma dagewarta na rura wutar yakin addini.”
Hamas ta kuma bukaci dukkanin kasashen Larabawa da na musulmi masu son ‘yanci da su kare masallacin Al-Aqsa daga fuskantar karuwar kutse.
Ministan na Isra’ila Ben-Gvir tare da wasu gungun ‘yan Isra’ila sun mamaye harabar masallacin Al-Aqsa da ke gabashin Quds da aka mamaye tare da gudanar da ayyukan ibada a harabar masallacin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara
Baya ga haka, Sojojin sun kashe ƙarin ‘yan ta’adda goma da suka taru kusa da wani gidan mai a Danjibga, waɗanda ake zargin sun kasance cikin wata tawagar da Dogo Sule ya tara domin kitsa hari. Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa rundunar Soji za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp