Tinubu ya bayyana cewa, aikin titin, wanda aka yi watsi da shi tuni duk da muhimmancin titin a cikin taswirar Abuja, amma yanzu ya kammalu a karkashin jagorancin Ministan babban birnin tarayya.

 

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya bai wa babban birnin tarayya zaman lafiya, da ci gaban Nijeriya, da kuma bai wa sojojin Nijeriya aminci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jagoranci zaman sasanci domin kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a garin Nahuta da ke Ƙaramar Hukumar Darazo.

Wannan sasanci na zuwa ne bayan makonni uku da aka shafe ana rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu.

Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman

A taron da aka yi a ranar Lahadi, gwamnan ya yaba da yadda dukkanin ɓangarorin suka fahimci juna.

Gwamna Bala, ya buƙaci jama’a da su guji duk wani abu da zai tayar da hankali, tare da yin kira a bin doka da oda.

Ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai domin hana rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

Taron ya samu halartar wakilan makiyaya da na manoma, ‘yan majalisa, shugabannin ƙananan hukumomi da na al’umma, ciki har da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Darazo da Ganjuwa.

A yayin taron, Gwamna Bala, ya sanar da kafa kwamitin bincike don gano dalilan rashin jituwa a tsakanin makiyaya da manoma.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ware hekta 2,500 na daji a domin ayyukan noma.

Ya nuna damuwarsa cewa wasu jami’ai da sarakunan gargajiya na raba filaye ba bisa ƙa’ida ba.

Gwamnan, ya gargaɗi manoma da ke karɓar filaye daga gwamnati amma suna bayar da su haya.

Ya ce: “Idan ba za ku yi noma da gonakin da aka ba ku ba, gwamnati za ta karɓe su ta bai wa waɗanda za su yi amfani da su.”

Ya ce gwamnati ba za ta amince da tashin hankali ba, kuma za ta ƙara ƙarfafa sasanci da tsaro domin samar da zaman lafiya.

Shugabannin Fulani, Malam Bala da Ahmadu Laddo, sun koka cewa manoma suna ƙoƙarin ƙwace filayen kiwo, kuma a wasu lokuta ana kai wa matansu hari.

Sun ce sun kai ƙara wajen ‘yan sanda da sarakunan gargajiya, amma babu abin da ya sauya.

Wakilan manoma, Mallam Lawal Babayo da mai unguwa Nadada, sun zargi makiyaya da kai musu hari da hana su noma a gonakin da gwamnati ta ware musu.

Wasu sun ce sun karɓi gonaki haya don noma, amma yanzu sun kasa noma, kuma hakan zai hana su samun amfanin gona.

Sun ƙara da cewa shekarun baya sun samu girbi mai yawa a gonakin da ke Darazo da Sade, amma bana rikici ya hana hakan.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sani Omolori, ya ce an tura jami’ai don tabbatar da doka da oda a yankin.

Masu jawabai a wajen taron sun yaba da matakin gwamnan, sun bayyana cewa wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen wanzar da zaman lafiya a Jihar Bauchi.

Sun roƙi a ci gaba da haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar sasancin.

 

Ga hotunan yadda taron ya gudana:

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Bukaci A Kara Inganta Aikin Titin Gabasawa
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Jimamin Rasuwar Babban Ɗan Jarida Leon Usigbe
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin Bai Wa Malaman Manyan Makarantun Nijeriya Rancen Miliyan 10
  • Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana
  • Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo
  • Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa
  • Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson
  • ADC Ga Tinubu: Ina Wutar Lantarki Ta Awa 24 Da Ka Yi Wa ‘Yan Nijeriya Alkawari?
  • Jihohin Da Ke Shirin Rage Kudin Wutar Lantarki Su Shirya Biyan Tallafi – Ministan Wuta
  • Fahimtar Sabon Tunani: Mene Ne Birnin Zamani Na Al’umma