Nan Ba Da Jimawa Ba Harkar Man Fetur Za Ta Sauya A Nijeriya – Dangote
Published: 11th, June 2025 GMT
Sai dai wasu daga cikin dillalan man fetur a Nijeriya na ganin ya kamata matatar ta riƙa sayar da lita ɗaya ƙasa da Naira 800, la’akari da cewa ana sayar mata da ɗanyen mai a kuɗin Naira maimakon Dala.
Dangote dai ya nuna ƙwarin guiwar cewa kamfaninsa zai taka rawar gani wajen samar da isasshen mai ga ‘yan Nijeriya tare da sauƙaƙa matsin da mutane ke ciki sakamakon hauhawar farashin fetur a ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato
Dakarun Runduna ta 3 ta ‘Operation Safe Haven’ masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a Ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a.
An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a ImoA cewar rundunar, kawun yaron ne ya sayar da shi shekaru uku da suka wuce.
Rundunar ta ce, an kuɓutar da yaron ne bayan wani samame da sojoji suka kai a maɓoyar miyagun da ke a Ƙaramar hukumar Riyom.
Da yake bayyana yadda aka kuɓutar da yaron, Manjo Zhakom ya ce “a ranar 22 ga Yuli, 2025, sojoji sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a lokacin da suka kai samame a maɓoyar ‘yan ta’adda a yankin Riyom.
“Bincike ya nuna cewa, kawunsa ne ya siyar da yaron shekaru 3 da suka gabata, amma an miƙa yaron ga Kansila mai wakiltar mazaɓar Zamko na Ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa a jihar Filato, wanda ake sa ran zai miƙa yaron ga danginsa,” in ji kakakin.
A wani labarin makamancin haka, rundunar ta ce dakarun sojin sun ƙwato makamai da alburusai a wani samame da suka kai a Ƙaramar hukumar Wase da ke jihar.
Manjo Zhakom ya bayyana cewa, “Bisa ga sahihan bayanan sirri da suka gano, ‘yan bindiga ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 a kan titin Kampani zuwa Kombodoro a Ƙaramar hukumar Wase ta Jihar Filato, sojojin sun yi kwanton ɓauna a kan hanyoyin ’yan fashi da ke kusa da unguwar Jeb.