Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Babban Darektan Hukumar IAEA Saboda Yadda Yake Mika Wuya Ga Bakar Siyasa
Published: 10th, June 2025 GMT
Babban darektan hukumar IAEA ya zama tamkar wata yar tsana ce a hannun kasashen Yamma don dakile shirin nukiliyar Iran
An fara taron kwata-kwata na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a birnin Vienna, wanda ya samu halartar wakilan kasashe 35 mambobi hukumar
Bisa la’akari da rahoton da babban daraktan ya fitar game da sa ido da tabbatar da shirin nukiliyar Iran karkashin yarjejeniyar kare kai da kuma tsarin aiwatar da ayyukan hadin gwiwa ta (JCPOA) na daya daga cikin batutuwan da za a tattauna.
Babban darektan hukumar ta IAEA Rafa’el Grossi ya sanar a wani rahoto da ya fitar a makon da ya gabata cewa; Yawan sinadarin uranium da Iran ke da shi ya ninka har kashi 60 cikin dari. Kamar yadda ya yi zargin samuwar wata makamashin nukiliya da Iran ba ta bayyana ba a baya, yana mai nanata batutuwan da aka rufe a baya a cikin matsalar da ya shafi harkar soji (PMD) tun a shekara ta 2015.
A martanin da Iran ta mayar a hukumance ta nuna rashin amincewarta da rahoton, inda ta bayyana shi da cewa ya kaucewa aikin fasaha na hukumar IAEA da kuma Sanya batun siyasa da nuna son kai. A cikin wata sanarwa da hukumar ta IAEA ta Iran ta aikewa hukumar ta IAEA ta duniya, ta yi watsi da wadannan zarge-zargen, tare da tabbatar da cewa babu wasu ayyukan nukiliya da ba a bayyana ba a kasar Iran, kuma shirin nukiliyar kasar na da cikakken gaskiya kuma yana karkashin kulawar hukumar ta IAEA ta duniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hukumar ta IAEA
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Tinubu Ya Rantsar Da Farfesa Dakas James Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki Ta Kasa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ɗakin taro na Majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.
Kafin a fara taron, Shugaban Ƙasa ya rantsar da Farfesa Dakas James Dakas da Dakta Uchenna Eugene a matsayin Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki ta Ƙasa da Kwamishina.
Majalisar ta kuma dakatar da taron na minti ɗaya domin girmama marigayi Cif Audu Ogbe, wanda ya kasance memba a majalisar a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari, haka kuma a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Cif Ogbe ya rasu a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, yana da shekaru 78.
Daga Bello Wakili