Iran: Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Tace Zata Maida Martani Kan Hukumar IAEA
Published: 11th, June 2025 GMT
Iran ta bada sanarwan cewa ta sharia matakan da zata dauka kan hukuma IAEA mau kula da makamashin nukliya ta duniya idan ta samar da kudurin yin allawadai ko kuma rashin bada ahadin kai ga hukumar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ik Baghae yana fadara haka a jiya Talata .
Baghae yayi allawadai da rahoton da Daraktan hukumar IAEA Rafael Grossi ya bayar dangane da shirin Nukliyar kasar kafin taron gwamnonin hukumar.
Yace wannan a fili ya nuna cewa hukumar AIEA tana aiki ne don dadadwa makiyan JMI wato Amurka da HKI. Grossi a rahotonsa ya bayyana cewa Iran ta ki ta bayyana ayyukan nukliyan da take yi a wurare uku a cikin kasar. Da kuma yadda ta tache makamancin Uranium har zuwa kashi 60%.
Ya kammala da cewa Iran ta dade tana shakkan ayyukan shugaban hukumar Makamashin nukliya ta IAEA, amma a cikin wasikun sirri da suka samu ta hanyar leken asiri sun tabbatar da abinda muke shakka.
Mohammad Eslamu daractan hukumar makamashin Nukliya ta kasar ya yi tir da rahoron grossi wanda a fili yana taimakawa maikan JMI a dai dai lokacinda yakamata a zama dan ba ruwammu ya daina shiga harkokin siyasa. Banda haka rahoton nasa bai da kima ga kwarraru wadanda suka san ayyukan makamashin nukliya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukliya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA