Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta sake jaddada aniyar ta na dakile yaduwar magungunan jabun a fadin kasar nan.

 

Darakta Janar na Hukumar Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye ta bayyana hakan a yayin bikin bude taron wayar da kan jama’a na kwanaki biyu da aka gudanar a Kano.

 

Farfesa Mojisola Christianah wacce Darakta Pharmacist, Pharmacist Bitrus Fraden ta wakilta ta ce NAFDAC ta bullo da wasu sabbin tsare-tsare guda uku da nufin inganta hanyoyin magance yaduwar magungunan jabu a kasar.

 

Babban Daraktan ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su tallafa wa wadannan tsare-tsare, da nufin tabbatar da samar da ingantattun kayayyakin kiwon lafiya, masu inganci ga ‘yan Nijeriya.

 

Ta ce Najeriya ita ce kasa ta farko a Afirka da ta fara amfani da wannan fasahar, wanda ke baiwa masu ruwa da tsaki damar ganowa da kuma watsi da kayayyakin da basu da inganci.

 

“Dokar hukumar kula da lafiyar yara ta NAFDAC mai lamba 2024 wata ka’ida ce ta musamman da ke magance bukatu na musamman na yara. Wannan ka’ida ta ginu ne a kan tsarin rijistar da ake da shi, yana ba da karin kariya don tabbatar da tsaro da ingancin kayayyakin kiwon lafiya ga yara.”

 

A nata bangaren wata mataimakiyar darakta Regina Garba ta ce makasudin taron shi ne wayar da kan masu ruwa da tsaki kan hadin gwiwa ta wannan fanni.

 

 

Ko’odinetan NAFDAC na shiyyar Arewa maso Yamma Mista Fadi Nantim Mullah ya ce makasudin gudanar da taron bitar a shiyyar ya kasance ne saboda yawaitar masu sana’ar magunguna musamman a Kano.

 

Abdullahi Jalaluddeen Kano

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa